Yan Igbo ba za su bari Buhari da APC su yaudaresu da shugabancin 2023 ba - Atiku

Yan Igbo ba za su bari Buhari da APC su yaudaresu da shugabancin 2023 ba - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar yace shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba za su cika alkawarin da suka daukarma kudu maso gabas na samar da shugaban kasa a 2023 idan suka marawa Buhari baya a shekara mai zuwa.

Atiku Abubakar yace shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba za su cika alkawarin da suka daukarma kudu maso gabas na samar da shugaban kasa a 2023 idan suka marawa Buhari baya a shekara mai zuwa.

Yace karara jam’iyyar APC na yaudarar yan Igbo ne saboda yayinda fadar shugban kasa ta babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ke fadin cewa shugabancin kasa zai kowa yankin kudu maso gabas, Babatunde Fashola, Ministan wutarantarki, ayyuka da gidaje yace ya kudu maso yamma ne za su yi shugabanci a 2023.

Yan Igbo ba za su bari Buhari da APC su yaudaresu da shugabancin 2023 ba - Atiku
Yan Igbo ba za su bari Buhari da APC su yaudaresu da shugabancin 2023 ba - Atiku
Asali: UGC

Atiku wanda yayi Magana tab akin Segun Sowunmi, kakakin kungiyar kamfen din shi, yace uhari da jam’iyyarsa sun nuna ceabasu da alkawari, wanda shine abunda suka daukarmayan Najeriya a lokacin kamfen din 2015 amma tsawon shekaru uku da rabi bayan nan shiru kawai ake ji.

Yace maimakon daukar alkawaran karya kamar na APC, ya nuna cewa shi yana yiwa yan gbo fatan alkhairi ta hanyar daukar dansu, Peter Obi a matsyin mataimakinsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shekarau, Yerima, Yayale na a fadar shugaban kasa don ganawa da Buhari

Atiku yace maimakon fafutuka kan yankin da zai haifar da shugaban kasa a 2023, kamata yayi yan Najeriya su mayar da hankali wajen sauya lamuran kasar domn awo ci gaba.

Ya kuma yi alkawarin ba kananan hukumomin gashin kasu domin su samu isasshen kudade da za su iya habbaka tushensu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel