Muna da bidiyon lokacin da sojoji ke kashe yan Shi’a da basu ji ba basu gani ba – New York Times

Muna da bidiyon lokacin da sojoji ke kashe yan Shi’a da basu ji ba basu gani ba – New York Times

- Jaridar New York Times tace tana da wani bidiyo da ke nuna jami’an rundunar sojoji a yayinda suke harbin mambobin kungiyar yan shia

- A kwanakin baya ne dai aka sha karo tsakanin jami’an tsaro day an shi’a da ke zanga-zangar a saki shugabansu

- New York Times tace hotuna da bidiyon da aka kwasa ya nuna akalla gawawwaki 26

Jaridar New York Times tayi ikirarin cewa tana da wani bidiyo da ke nuna jami’an rundunar sojoji a yayinda suke harbin mambobin kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a wanda basu jiba basu gani ba sannan ba wai suna da makamai bane.

A cewar New York Times, bidiyon na nuna sojoji a lokacin das ka budema yan kungiyar wuta inda suke ta harbi ba kakkautawa a cikin dandazon yan kungiyar yayinda mutane suka tsere don tsirar da rayuwarsu.

Muna da bidiyo lokacin da sojoji ke kashe yan Shi’a da basu ji ba basu gani ba – New York Times
Muna da bidiyo lokacin da sojoji ke kashe yan Shi’a da basu ji ba basu gani ba – New York Times
Asali: UGC

Tace hotuna da bidiyon da aka kwasa ya nuna akalla gawawwaki 26. Kungiyar Shi’a tace ta samu gawawwaki 49 na wadanda aka kashe a zanga-zangan kwanaki hudu.

KU KARANTA KUMA: Hadimin Gwamna Obiano ya jagoranci kamfen din Buhari a kudu maso gabas

Mai karatu dai zai iya tuna cewa gwamnatin ta tarayyar Najeriya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ce ke cigaba da tsare shugaban 'yan shi'ar Sheikh Ibrahim Zakzaky biyo bayan wata arangaba da mabiyan sa suka yi da jami'an tsaro a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel