Duniya na kallo ku na zubar wa Najeriya mutunci - Buhari ga yan majalisa

Duniya na kallo ku na zubar wa Najeriya mutunci - Buhari ga yan majalisa

- Shugaba Buhari ya ja hankalin yan majalisar dokokin da su guji tozarta kasar a duk lokacin da duniya ke kallon abin da ke gudana a zauren majalisar

- Buhari ya bayyana hakan ne cikin sigar ban tausayi bayan tozarcin da ya fuskanta daga wasu mambobin majalisar a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kudin 2019

- Wasu yan majalisar dai suka rika yi masa ihu da sowa da furta ba ma yi, ba mayi. Wasu ma sun rika wuce gona da iri, su na karyata shi

Rahotanni sun kawo cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ja hankalin yan majalisar dokokin tarayya da su guji tozarta kasar ajeriya a duk lokacin da duniya ke kallon abin da ke gudana a zauren majalisar.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin sigar ban tausayi bayan tozarcin da ya fuskanta daga wasu mambobin majalisar a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kudin 2019.

Duniya na kallo ku na zubar wa Najeriya mutunci - Buhari ga yan majalisa
Duniya na kallo ku na zubar wa Najeriya mutunci - Buhari ga yan majalisa
Asali: Depositphotos

Wasu yan majalisar dai suka rika yi masa ihu da sowa da furta ba ma yi, ba mayi. Wasu ma sun rika wuce gona da iri, su na cewa karya ce.

A cikin tattausar zuciya, shugaba Buhari ya roki mambobin da su daina abin da suke yi, domin duniya gaba daya na kallon abin da ke faruwa.

KU KARANTA KUMA: Yadda Gwamnatin Buhari ta shirya kashe Tiriliyan 8.83 a shekara mai zuwa

Buhari ya shaida musu cewa wannan ne kasafin kudi na karshe da zai gabatar wa majalisar a wannan zango na sa.

A halin da ake ciki, mun ji labari cewa shugaban majalisar dattawa na Najeriya, Bukola Saraki, yayi wani jawabi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kundin kasafin kudin 2019 a gaban ‘Yan Majalisar Tarayya jiya a Garin Abuja.

Bukola Saraki ya nuna cewa har yanzu tattalin arzikin Najeriya yana rawa inda ya alakanta wannan matsala da karyewar farashin gangar man fetur a fadin Duniya. Saraki yace rugujewar tattalin arzikin da aka samu ya taba kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel