Yawan kudin da yan Najeriya ke kashewa wajen tafiya karatu a kasashen waje duk shekara

Yawan kudin da yan Najeriya ke kashewa wajen tafiya karatu a kasashen waje duk shekara

Shugaban Jami’ar Crawford, kuma tsohon Shugaban Jami’ar Lagas, Farfesa Oye Ibidapo-Obe, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na kashe kimanin naira tiriliyan daya a duk shekara wajen tafiya kasashen waje domin yin karatun digiri.

Farfesa Oye Ibidapo-Obe, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na kashe kimanin naira tiriliyan daya a duk shekara wajen tafiya kasashen waje domin yin karatun digiri

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 12 ga watan Disamba yayinda ya ke jawabi a bikin yaye dalibai karo na 10 na Jami’ar Crawford da ke garin Igbesa, jihar Ogun.

Yawan kudin da yan Najeriya ke kashewa wajen tafiya karatu a kasashen waje duk shekara
Yawan kudin da yan Najeriya ke kashewa wajen tafiya karatu a kasashen waje duk shekara
Asali: UGC

Ya tona yadda ake kashe wadannan makudan kudade ne, daidai lokacin da malaman jami’o’in Najeriya ke ci gaba da gudanar da yajin aikin da suka fara tun daga ranar 4 ga watan Nuwamba.

Daga nan ya ci gaba da nuna muhimmancin ci gaba da kafa jami’o’i masu zaman kan su wadanda ba na gwamnati ba.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin kasa: Abokin takarar Donald Duke ya janye daga tseren

Ya ce ta haka ne za su kara samun ingancin da za a rage karakainar neman karin ilmi a kasashen duniya, inda ake kwasar makudan kudade ana tafiya da sunan tafiya karin ilmi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng