Kasafin 2019: Kakakin majalisar Adamawa ya yabama Buhari kan ware wa arewa maso gabas N45b

Kasafin 2019: Kakakin majalisar Adamawa ya yabama Buhari kan ware wa arewa maso gabas N45b

- Kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa ya yabama Buhari kan ware wa yankin arewa maso gabas N45b

- Mijinyawa yace idan har aka amince da kason da aka ware domin ci gaban yankin babu shakka zai gyara da inganta barnar da yan ta’adda suka yi a yankin

- Ya ba Buhari tabbacin cewa mutanen yankin za su saka masa da karamcin da yayi maso ta hanyar mara masa baya a 2019

Kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Alhaji Kabiru Mijinyawa, ya yaba ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan ware naira biliyan 45 cikin kasafin kudin 2019 domin ci gaban yankin arewa maso gabas.

Mijinyawa ya yabama shugaban kasar ne a wani hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Yola.

Ya bayyana cewa idan har aka amince da kason da aka ware domin ci gaban yankin arewa maso gabas babu shakka zai inganta ta’addin da yan ta’adda suka yi a yankin idan har aka bi dashi yadda ya kamata.

Kasafin 2019: Kakakin majalisar Adamawa ya yabama Buhari kan ware wa arewa maso gabas N45b
Kasafin 2019: Kakakin majalisar Adamawa ya yabama Buhari kan ware wa arewa maso gabas N45b
Asali: Facebook

Kakakin majalisar wanda ya nuna karfin gwiwa da gwamnatin Buhari ya kuma yaba ma kokarin shugaban kasar domin bunkasa yankin, musamman aikin yin manyan tituna a jihar.

Ya bayyana cewa aikin hanyar Mayo-Belwa-Jada-Ganye da Toungo na biliyan 22 na daga cikin manyan nasarorin da aka samu a karkashin gwamnatin Buhari.

KU KARANTA KUMA: PDP ta tarbi masu sauya sheka daga APC da ADP a Niger

Mijinyawa ya ba shugaban kasar tabbacin cewa mutanen jihar za su saka masa akan wannan karamci da yayi masu ta hanyar goya masa baya a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel