Atiku, Obi sun gana da kungiyoyin jama’a, sun amince da hada kai don damokradiyya

Atiku, Obi sun gana da kungiyoyin jama’a, sun amince da hada kai don damokradiyya

Dan takarar kujeran shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa; PDP, a raar 2 ga watan Disamba ya gana da mambobin kungiyoyin jama’a. Alhaji Atiku da mataimakinsa, Mista Peter Obi, sun samu rakiyan manyan mamabobin jam’iyyar kamar irin su shugaban jam’iyyar Prince Uche Secondus, shugaban majalisar dattawa wanda kuma shine shugaban kamfen dinsa, Abubakar Bukola Saraki, Sanata Dino Melaye da sauran mambobin kungiyoyin jama’a irinsu Alhaji Buba Galadima da kuma jarumin Nollywood,Bob Manuel Udokwu.

Atiku, Obi sun gana da kungiyoyin jama’a, sun amince da hada kai don damokradiyya

Ana ganin wanan ganawar na da matukar muhimmanci tunda mambobin kungiyoyin jama’a da dama na ganin sun zamo Karen farautar gwamnatin Buhari, ciki harda kungiyar Amnesty International. A ganawar wasu mambobin kungiyoyin jama’a da suka yi magana sun sake tabbatar da rawar ganin kungiyar a matsayin na uku a kasar.

Alhaji Buba Galadima, tsohon dan kashenin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da hakuri akan goyon bayan shugaba Buhari a baya inda ya bayyana cewa “wannan ba shine Buhari da muka sani ba.”

Atiku, Obi sun gana da kungiyoyin jama’a, sun amince da hada kai don damokradiyya

Dr. Abubakar Bukola Saraki a jawabinsa bai bar kowani bangare ba tare da ya taba ba yayinda ya kalubalanci kasafin kudin 2019 da shugaba Buhari ya gabatar, inda ya bayyana cewa “wannan kasafin kudin bai da wani tanadi ga kowa”, bayan zarge-zarge da dama kan cewa gwamnatin Buhari tayi ikirarin kammala ayyukan da basu kammalu ba a kasafin kudin.

Akan rigimar dokar zabe, shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa “INEC ta fada mana cewa basu da isashen lokacin yin aiki da gyararren dokar zaben, shugaban kasar bai da wani uzuri.”

Atiku, Obi sun gana da kungiyoyin jama’a, sun amince da hada kai don damokradiyya

Mista Bob Manuel Udokwu yayi Magana kan zuba jari da dama a lokacin PDP a Nollywood. Ya bayyana karara “PDP da Jonathan sune gwamnatin farko da suka zuba jari a masana’antar. Ya kai wani lokaci da Nollywood ya zamo na biyu wajen diba ma’aikata, yanzu Nollywood ya zama tsit."

Wannan misali ne ga hiran da Miss Genevieve Nnaji tayi kwanan nan da CNN, inda ta bayyana cewa ita ta dauki nauyin finm dinta na Lionheart, ba kamar sauran wurare ba da gwamnati ke samar da wasu yan kayayyaki ga ma’aikatar fina-finansu. Mista Bob Manuel ya ci gaba da bayyana dalilin da yasa zama dole yan Najeriya su marawa PDP baya don ta dawo mulki saboda PDP ta dauki maganar da gaskiya da tace zata samar da ayyuka.

Atiku, Obi sun gana da kungiyoyin jama’a, sun amince da hada kai don damokradiyya

Mista Peter Obi, wanda Sanata Dino Melaye ya bayyana a matsayin mutumin da zai kawo ci gaba a rayuwar al’umma, yayi magan kan abubuwan da ke damun Najeriya. Mista Obi caccaki sigar da gwamnatin Buhari ta dauko ayyukan ci gaba, “Sun fada maku cewa suna ta aron kudaden ayyuka, wani aiki ne yafi na abban titin Lagas zuwa Ibadan muhimmanci? Nawa suka saki don haka?.

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutane 5 a Zamfara

Atiku, Obi sun gana da kungiyoyin jama’a, sun amince da hada kai don damokradiyya

Akan ikirarin gwamnatin tarayya na cewa babu kudi a Najeriya don ayyukan ci gaba, Mista Obi ya tabbatar, “mutane na ta tambaya-Peter, a ina zaka samo kudin wadannan ayyukan da kake Magana a kai.” Mista Obi ya fadi abubuwa da dama kan yadda bankin masana’’anta wanda ya kamata ya dauki nauyin dukkanin masana’antu ya tagayyara ya zama katramin banki.

Alhaji Atiku Abubakar ya shigo wajen taron da farinciki sosai, ya samu rakiyan shugaban jam’iyyar PDP. Yayi Magana cikin sigar ban tausayi game da aiki tare da kungiyoyin jama’a domin tabbatar da damokradiyya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel