Bikin cika shekara 76: Ka koma Daura ka huta – PDP ga Buhari

Bikin cika shekara 76: Ka koma Daura ka huta – PDP ga Buhari

- Jam’iyyar PDP ta shawarci shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya koma gidansa a Daura domin ya huta da kyau

- Hakan martani ne ga rokon da shugaba Buhari yayi na cewa a kara masa lokaci domin ya gyara kasar

- PDP tace ba za’a ba mutumin da aka nemi yaje ya wuta koda yaushe aikin dawo da kasar kan tafarki na gari ba

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Litinin, 17 ga watan Disamba ta shawarci shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya koma gidansa a Daura domin ya huta da kyau.

Da suke mayar da martani ga rokon Buhari na cewa a kara masa lokaci domin ya gyara kasar, PDP tace ba za’a ba mutumin da aka nemi yaje ya huta koda yaushe aikin dawo da kasar kan tafarki na gari ba.

Babban sakataren labarai na jam’iyyar, Mista Kola Ologbondiyan ya fadama majiyarmu ta Punch cewa shugaban kasar ya koma gidansa na Daura, jihar Katsina, inda yace shugaban kasar zai samu hutun da ya cancanta.

Bikin cika shekara 76: Ka koma Daura ka huta – PDP ga Buhari

Bikin cika shekara 76: Ka koma Daura ka huta – PDP ga Buhari
Source: Depositphotos

A cewarsa babu lokacin batawa kasar ba zata ci gaba da kasancewa a hannun shugaban kasa mai bacci ba.

KU KARANTA KUMA: Ma’aikata sun yanke wuta da hanyar ruwa na majalisar dokokin kasar

Yace shugaba Buhari yayi abunda zai iya yi amma sai dai kokarinsa bai ishi kasar ba ko kadan.

Ologbodiyan yace ya kamata shugaban kasar ya dauki shawarar likitocinsa day ace sunce ya huta, yaci abinci sannan ya dunga bacci sosai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel