Jam’iyyar APM za ta fara kamfen, ta amince da Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa

Jam’iyyar APM za ta fara kamfen, ta amince da Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa

- Jami’iyyar APM babin jihar Ogun za ta fara kamfen dinta a yau Alhamis

- Ta kuma amince da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zabe mai zuwa

Jami’iyyar Allied People’s Movement (APM) babin jihar Ogun za ta fara kamfen dinta a yau Alhamis, 20 ga watan Disamba, sannan ta amince da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Za kuma tayi amfani da wannan damar wajen gabatar da Hon. Adekunle Akinlade, wanda Gwamna Ibikunle Amosun ya fi so a matsayin dan takarar gwamnan jam’iyyar a jihar tare da mataimakinsa Adepeju Adebajo.

Jam’iyyar APM za ta fara kamfen, ta amince da Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa

Jam’iyyar APM za ta fara kamfen, ta amince da Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa
Source: Facebook

Yayinda mambobin jam’iyyar da magoya bayansu ke shirin zabar Akinlade a matsayi gwamna a zabe mai zuwa, sun yanke shawarar zabar Shugaba Buhari a matsayin dan takararsu na shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da nadin sabuwar mai shari'a na kotun koli

Akinlade wanda ya sauya sheka kwanan nan daga am’iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana APM a matsayin jam’iyyar da zata ci gaba akan tafarkin gwamnan jihar mai ci Ibikunle Amosun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel