Rikicin cikin gida: Baki isa ki rushe mu ba – APC babin Ogun ga uwar jam’iyya

Rikicin cikin gida: Baki isa ki rushe mu ba – APC babin Ogun ga uwar jam’iyya

- Jam’iyyar APC a jihar Ogun ta yi watsi da rusheta da uwar jam’iyyar tayi

- Mun dai ji hukuncin uwar jam’iyya karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, na rushe jam’iyyar APC a dukkanin mataki a jihar Ogun

- Shugaban APC babin jihar, Derin Adebiyi, ya bayyana lamarin rushewar a matsayin tatsuniya cewa lamarin na gaban babban kotu

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ogun ta yi watsi da rusheta da uwar jam’iyyar tayi.

Legit.ng ta rahoto a baya hukuncin uwar jam’iyya karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, na rushe jam’iyyar APC a dukkanin mataki a jihar Ogun.

Rikicin cikin gida: Baki isa ki rushe mu ba – APC babin Ogun ga uwar jam’iyya

Rikicin cikin gida: Baki isa ki rushe mu ba – APC babin Ogun ga uwar jam’iyya
Source: Depositphotos

Jam’iyyar APC jihar Ogun na biyayya ga gwamnan jihar, Ibikunle Amosun wanda suka shiga kafar wando daya da Oshiomhole tun bayan rigiman da aka yi a zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Sakataren Yada Labarai a APC na Kasa, Lanre Issa-Onilu ya tabbatar da lamarin rushewar a yau Laraba, 19 ga watan Disamba.

Ana zargin shugabannin da aka rusa din duk su na goyon bayan gwamnonin ne, wadanda su kuma gwamnonin ba su goyon bayan jam’iyyar su ta APC ta yi nasara a zaben gwamna a jihar su.

KU KARANTA KUMA: APC ta ruguza duka shugabannin ta a Jihohin Imo da Ogun

Da yake martani akan lamarin rushewar, shugaban APC babin jihar, Derin Adebiyi, ya bayyana lamarin rushewar a matsayin tatsuniya cewa lamarin na gaban babban kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel