Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe 14 sun kuma raunata 17 a kauyen Kaduna

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe 14 sun kuma raunata 17 a kauyen Kaduna

- Yan bindiga sun kai hari a kauyen Unguwan Paa-Gwandara da ke karamar hukumar Jema’a na jihar Kaduna

- Sun kashe mutane 14 sannan sun raunata 17 a daren ranar Lahadi, 16 ga watan Disamba

- Hakazalika, Misis Victoria Martins, wata da ke samun kulawa a babban asibitin Kafanchan ta bayyana cewa mata da yara abun ya fi shafa

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe mutane 14 sannan sun raunata 17 a daren ranar Lahadi, 16 ga watan Disamba a kauyen Unguwan Paa-Gwandara da ke karamar hukumar Jema’a na jihar Kaduna.

Mista Joshua Paul, wani mazaunin garin ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kafanchan a ranar Litinin cewa wadanda abun ya cika da su na a wajeen biki lokacin da aka kai masu harin da misalin karfe 8 na dare.

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe 14 sun kuma raunata 17 a kauyen Kaduna
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe 14 sun kuma raunata 17 a kauyen Kaduna
Asali: Depositphotos

“Mutane tara aka kashe anan take yayinda biyar suka mutu da safiyar yau a babban asibitin Kafanchan.

“Wasu 17 ciki harda yara shida sun ji mumunan rauni na harbion bindiga sannan kuma suna cikin wani hali,” inji shi.

Hakazalika, Misis Victoria Martins, wata da ke samun kulawa a babban asibitin Kafanchan ta bayyana cewa mata da yara abun ya fi shafa.

KU KARANTA KUMA: Mun yi nadamar zaben Buhari - Kungiyar matasan arewa

Da yake tabbatar da lamarin, shugaban karamar hukumar Jema’a, Mista Peter Averik ya bayyana cewa ba’a riga an koro masa cikakken bayani akan lamartin ba amma tuni an tura yan sanda inda abun ya faru.

Ba’a samu jin tab akin yan sanda ba amma wata majiya tace rundunar zata koro jawabi daga nan gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel