Gudaji Kazaure ya kwancewa 'yan PDP zani a kasuwa kan Buhari

Gudaji Kazaure ya kwancewa 'yan PDP zani a kasuwa kan Buhari

- Gudaji Kazaure ya caccaki jam’iyyar PDP da mambobinta na majalisar dokokin kasar da suka nuna tirjiya a yayinda shugaba Buhari ke gabatar da kasafin kudin 2019

- Yayi zargin cewa yan PDP na bakin ciki ne da ci gaban da shugaban kasar ke kokarin kawowa a rayuwar talakawan kasar

- Yace wajibi ne majalisar tamince da kasafin kudin da Buhari ya gabatar

Honourable Gudaji Kazaure ya caccaki jam’iyyar PDP da mambobinta na majalisar dokokin kasar da suka nuna tirjiya a yayinda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke gabatar da kasafin kudin 2019.

A yau Laraba, 19 ga watan Disamba ne shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin a majalisun dokokin kasar.

Sai dai an dan samu tsaiko lokacin da wasu yan majalisa suka yi ihu don tozarta shugaban kasar.

Gudaji yayi zargin cewa yan PDP na bakin ciki ne da ci gaban da shugaban kasar ke kokarin kawowa a rayuwar talakawan kasar.

Gudaji Kazaure ya kwancewa 'yan PDP zani a kasuwa kan Buhari

Gudaji Kazaure ya kwancewa 'yan PDP zani a kasuwa kan Buhari
Source: UGC

Yace: “Abunda ya faru abun kunya ne ga jam’iyyar PDP duba ga yadda sukan lalata shekarun 16 da suka yi suna mulki

“Buhari na iya bakin kokarinsa don farfado da barnar da suke mana amma suke kokarin sai sun nuna gazawarsa.

“Tunma shugaban kasar bai zo suka shirya cewa sai sun yi masam ihu amma mu muka ce duk wanda yayi masa ihu sai bayan ranmu.

“Don mutum hamsin sun yi ihu ba komai bane cikin mutane 500, cewa hakan ba komai bane sai adawar siyasar.

KU KARANTA KUMA: Ku yi murabus yanzu ku shugabannin marasa rinjaye ne - Akpabio ga Saraki da Dogara

“Bakin ciki suke yi don Buhari kada yayiwa talakawa aikin ci gaba shiyasa suke kawo cikas.”

Da aka tambaye shi ko yan PDP da APC za su iya amince da kasafin kudin ganin yadda kawunansu ya rabu Gudaji yace: “Sai dai mu daku akan wannan kasafin kudin, kai ni kadai zan mike nace nayi yarda da kasafin kudin a madadin majalisar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel