Ahmad Yusuf
11628 articles published since 01 Mar 2021
11628 articles published since 01 Mar 2021
Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kauda kai daga masu kokarin ɗauke masa hankali, ya yi wa al'umma aiki a Kano.
Jam'iyyar APC reshen shiyyar Kudu maso Kudu ta bayyana goyon bayanta ga Bola Ahmed Tinubu, ta nemi sake tsayawa takara a zaɓen shugaban masa na 2027.
Wasu ɓata gari sun sace ragon da babban limami ya sayo da nufin yin layya a yankin ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato, lamarin ya faru ranar jajibiri.
Rundunar sojin saman Najeriya ta samu nasarar ragargazar ƴan bindiga sama da 100 a wani samame da jirgin yaƙin sojojin da kai sansanin ƴan bindiga a yankin Faskari.
Wasu matasa sun tada hargitsi a wurin naɗin sabon basaraken Nkomoro a ƙaramar hukumar Ezza ta Arewa da ke jihar Ebonyi, sun lalata motocin jami'ai.
Gwamnatin tarayya ta sake tura tan sama da 2,000 na kayan masarufi ga gwamnatin jihar Kano domin a rabawa talakawa da marasa ƙarfi a kananan hukumomi 44.
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta ce za ta sanar da hukuncinta kan bukatar da ta nemi soke sabuwar dokar masarautar Kano da Gwamna Abba Kabir ta yi.
Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya rattaba hannu kan kudirin sauya sunan jami'ar jihar da ke Gadau zuwa Jami'ar Sa'adu Zungur (SAZU), Gadau.
Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna ta sanar da rasuwar Hajiya Amina Muhammad Ladan a asibitin King Fahad da ke birnin Makkah a ƙasar Saudiyya.
Ahmad Yusuf
Samu kari