Zaben 2027: Rigima Ta Yi Zafi tsakanin Gwamnatin Kebbi da Abubakar Malami

Zaben 2027: Rigima Ta Yi Zafi tsakanin Gwamnatin Kebbi da Abubakar Malami

  • Gwamnatin Kebbi ta buƙaci ɗan takarar gwamna na ADC, Abubakar Malami, da ya dakatar da abin da ta kira yaƙin ɓata mata suna
  • Kwamishinan Yaɗa Labarai, Yakubu Ahmed, ya musanta cewa gwamnati ta bayar da umarnin rushe wani fili a kan hanyar bypass ta Birnin Kebbi
  • Gwamnatin ta buƙaci Malami da jam’iyyarsa su janye zarge-zargen da ta kira ƙarya tare da ba da haƙuri, ko su fuskanci matakin shari’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Gwamnatin Jihar Kebbi ta gargaɗi ɗan takarar gwamna na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar, Abubakar Malami.

Gwamnatin ta gargadi Abubakar Malamai da ya dakatar da abin da ta kira yaƙin ɓata mata suna da Gwamna Nasir Idris.

Gwamnatin Kebbi ta ja kunnen Abubakar Malami
Abubakar Malami da gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris Hoto: Abubakar Malami, SAN, Dr Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Alhaji Yakubu Ahmed, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

"Nan ba da daɗewa ba yan Najeriya za su fara murna da tsare tsaren Shugaba Tinubu"

Ya kuma musanta zargin cewa gwamnatin jihar ce ta bayar da umarnin rushe wani fili da ke kan hanyar zagaye birnin (bypass), wanda ake zargin na wani abokin hulɗar Malami ne.

Gwamnati ta musanta hannu a rushe filin

Yakubu Ahmed ya ce gwamnatin jihar ba ita ce mamallakin filin da ake takaddama a kansa ba, kuma ba ta ba kowa izinin rushe shi ba.

Ya bayyana cewa mai filin, Alhaji Ummaru Gulumbe, ya riga ya yi bayanin matsayinsa kan rikicin da ya shafi mallakar filin.

Kwamishinan ya nuna mamakinsa kan dalilin da ya sa ɗan takarar gwamnan na ADC da jam’iyyarsa suka danganta gwamnatin jihar da takaddamar filin.

Ya kuma yi zargin cewa jam’iyyar ta yi ikirarin cewa ginin ofishinta ne gwamnatin ta rushe, duk da cewa gwamnati ta musanta hannu a lamarin.

Gwamnati ta buƙaci Malami ya janye zarge-zarge

Gwamnatin Kebbi ta buƙaci tsohon ministan da jam’iyyarsa da su janye abin da ta bayyana a matsayin zarge-zargen ƙarya da kalaman da suka yi kan gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Sabon umarnin da APC ta ba ministoci da masu mukamai kan kamfen din Tinubu

Ta kuma buƙaci su bayar da haƙuri, tare da gargaɗin cewa za ta ɗauki matakin shari’a idan suka ƙi yin hakan.

Yakubu ya zargi Malami da amfani da duk wata dama wajen nuna gwamnatin Kebbi cikin mummunan yanayi, domin samun goyon bayan masu zaɓe a jihar.

Kwamishinan ya ce:

“Muna so mu bayyana wa tsohon ministan da jam’iyyarsa cewa dole ne su janye ikirarin ƙaryarsu dangane da rushe filin da kuma kalaman da suka yi kan gwamnati, ko kuma su fuskanci matakin shari’a.”

An gargaɗi Wambam Koko kan kalamansa

Kwamishinan ya kuma gargaɗi wani abokin huldar Malami mai suna Wambam Koko da ya daina kai wa Gwamna Nasir Idris hare-haren baka ba tare da wani dalili ba.

Ya yi wannan gargaɗin ne a cikin martanin gwamnatin jihar kan kalaman da ake zargin Wambam Koko na yi wa gwamnan.

Gwamnatin Kebbi ta gargadi Malami
Gwamna Nasir Idris a wajen taro Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Abubakar Malami ya kai kara a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Abubakar Malami SAN ya shigar da ƙara a gaban kwamishinan ’yan sandan jihar Kebbi kan rushe gininsa a Birnin Kebbi.

Tsohon Babban lauyan na Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a a lokacin Muhammadu Buhari ya kai batun gaban hukuma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng