Rashin tsaro: Gwamnati ta kawo yadda za ta yi maganin hare-hare a makarantun Zamfara

Rashin tsaro: Gwamnati ta kawo yadda za ta yi maganin hare-hare a makarantun Zamfara

  • Za a aika Jami’an tsaro zuwa duk wata makarantar boko da ke jihar Zamfara
  • Gwamna Bello Matawalle ya yi wannan bayani a gidan gwamnati da ke Gusau
  • Matawalle ya kuma yi alkawarin inganta harkar ilmi musamman na yara mata

Gusau - Hukumomi na jihar Zamfara sun kammala shirye-shirye domin baza jami’an tsaro a duka wasu makarantu da ke jihar domin kare malamai da dalibai.

A wani rahoto da gidan talabijin na Channels TV ya fitar, an ji cewa gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, 2021.

Mai girma gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da wasu dalibai a gidan gwamnati da ke babban birnin Gusau.

Read also

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Gwamnan bai yi bayanin yadda za a aika jami’an tsaro zuwa kowace makaranta da ke jihar ba. Sannan bai bayyana wasu jami’an da za a ba wannan aikin ba.

Gwamnatin Matawalle za ta inganta ilmi

Rahoton yace Bello Matawalle ya sha alwashin cewa zai tsare al’umma. Sannan gwamnan ya yi alkawari gwamnatin jiha za ta bada kasonta a UBEC a bana.

Gwamna Matawalle yace zai yi wannan domin bunkasa ilmi a jihar Zamfara, musamman na ‘ya ‘ya mata.

Gwamnan Zamfara
Gwamna Bello Matawalle na Zamfara Hoto: pdpgovernorsforum.com
Source: UGC

Zainab Bello ta zama Gwamna

Domin bikin ‘ya ‘ya mata na Duniya, gwamnan ya sauka daga kujerarsa, ya damka wa wata dalibar sakandare a makarantar Kwatarkwashi, Zainab Bello.

Yayin da ta ke kan kujerar gwamna, Zainab wanda take aji biyu a sakandare ta tura Kwamishina Fa’ika Ahmed zuwa ma’aikatar bada tallafi da walwalar al’umma.

Read also

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

Sabuwar kwamishinar da aka zaba, Fa’ika Ahmed ta yi alkawarin taimaka wa wajen bunkasa ilmin ‘ya ‘ya mata, kamar yadda yake cikin tsarin Bello Matawalle.

Zamfara na fama da matsalar tsaro, shi ya sa da yake nada sababbin kantomomi a jihar Zamfara, Matawalle ya sake jaddada cewa burinsa shi ne kawo zaman lafiya.

'Yan majalisa suna da alaka da 'yan bindiga?

Kwanan nan aka ji majalisar Zamfara ta dakatar da wasu 'ya 'yanta kan zargin alaka da 'yan bindiga.

Honorabul Muhammad Yusuf, mai wakiltar Anka a majalisar dokokin Zamfara ya musanta zargin da ake yi masa, ya kuma bayyana abin da ya jawo aka masa sharri.

Source: Legit

Online view pixel