Da ƙyar muke numfashi: Ƴan majalisar tarayya sun buƙaci a yi gaggawar gyara musu na’urar sanyaya wuri ta AC

Da ƙyar muke numfashi: Ƴan majalisar tarayya sun buƙaci a yi gaggawar gyara musu na’urar sanyaya wuri ta AC

  • ‘Yan majalisar wakilai a ranar Talata sun koka akan azabar zafin da ya barke mu su a majalisar
  • Dan majalisar, Haruna Dederi ya bukaci a yi duba kuma ayi gaggawar gyara musu na’urar sanyaya wuri ta AC
  • Kamar yadda ya yi korafi, ko dai su hakura da zaman majalisa a yau ko kuma a yi gaggawar gyara musu AC din

Abuja - Majalisar wakilai na Tarayya a ranar Talata ta yi gaggawar datse zamanta sakamakon korafin da ‘yan majalisar su ka dinga yi akan azababben zafin da ke majalisar.

Wani dan majalisar, Haruna Dederi, dan jam’iyyar APC daga Kano, ya bukaci a dage zaman majalisar.

Da ƙyar muke numfashi: Ƴan majalisar tarayya sun buƙaci a yi gaggawar gyara mu su na’urar sanyaya wuri ta AC
An yi gaggawar datse zaman majalisa saboda rashin na'urar AC. Hoto: Vanguard Ngr
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

Yayin da yake daga maganar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito, ya ce:

“Ranka ya dade, doka ta 7 ta gidannan ta ba mu damar samun cikakken iko dangane da samun natsuwa yayin zama a majalisar nan.”
“A samar mana da cikakkiyar natsuwa wurin yin ayyukan da su ka dace. Saboda a halin yanzu muna wahala sakamakon azababben zafin da majalisar nan take da shi.
“A tawa shawarar, ya kamata a dage mana zaman yau ko kuma a yi gaggawar gyara na’urar sanyaya wuri ta AC dake majalisar nan.
“Duk yadda za ayi, a yi kokarin yi don samar mana da natsuwa a cikin majalisar nan".

Kakakin majalisar ya ce abin duba wa ne

Yayin da kakakin majalisa ya yi nazari akan maganar ta Dederi, bisa ruwayar Vanguard cewa ya yi:

“Wannan maganar gaskiya ce, kuma yanzu mu ka gama tattaunawa da mataimaki na a kai.
“Ina ganin abinda za ayi shi ne kowa ya tafi ya yi sallah, in ya so sai mu sanya wannan batun a matsayin mahawara don samun hanyar da za a bullo wa lamarin da sauri.

Read also

Dan majalisa ga FG: Makuden kudi kafintoci da direbobi ke samu, a wajabta musu haraji

“Mun dauki wannan batu kuma kowa zai iya tafiya.”

Ranar Talata ce rana ta biyu da majalisar ta tayar da zaman ta sakamakon yadda ‘yan majalisar su ke a takure yayin zama a majalisar.

Source: Legit

Online view pixel