Allah ne mai bada mulki, kuma yana bada shi ga wanda ya so, a lokacin da ya so, Tinubu

Allah ne mai bada mulki, kuma yana bada shi ga wanda ya so, a lokacin da ya so, Tinubu

  • Jigon jam'iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, yace Allah ne kaɗai ke da ikon baiwa bawansa mulki a lokacin da ya so
  • Tsohon gwamnan Legas ya kara da cewa idan Allah ya baka mulki, to ya baka wata dama ce da zaka kyautatawa Al'umma
  • Tinubu ya bayyana tsantsar jin daɗinsa da kuma godiya bisa yadda yan Najeriya suke nuna masa ƙauna da kulawa yayin da yake ƙasar waje

Lagos - Jigon jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, yace Allah ne mai bada mulki ga wanda yaso kuma a lokacin da ya so, kamar yadda Premiun times ta ruwaito.

Tinubu ya yi wannan furucin ne a Legas ranar Lahadi, yayin da ya sake haɗuwa da abokanan siyasarsa da ɗumbin mgoya bayansa a wurin liyafar maraba da kuma addu'a, wanda gwamna Sanwo-Olu ya shirya masa.

Read also

Allah kadai zai iya daukar rayuwa ta: Tinubu ya gana da mukarrabansa

Taron liyafar ne na farko da Tinubu ya halarta tun bayan dawowarsa daga birnin Landan, ranar Jumu'a da daddare, inda ya shafe watanni uku.

Bola Tinubu
Allah ne mai bada mulki, kuma yana bada shi ga wanda ya so, a lokacin da ya so, Tinubu Hoto: Punchng.com
Source: UGC

Ana hasashen dai Bola Tinubu, na ɗauke da kudirin neman takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen dake tafe na shekarar 2023 karkashin APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abinda ake tsammani idan Allah ya baka mulki?

Jigon jam'iyyar APC yace a koda yaushe idan Allah ya baka dama, to yana tsammanin ka yi amfani da wannan damar wajen kyautatawa mutane.

Yace yaji daɗin wannan taron na yi masa addu'a musamman yadda yan Najeriya suka rinka masa fatan alkairi lokacin da baya ƙasa.

Tinubu yace:

"Duk addu'ar da yan Najeriya suke mana, tana tasiri akaina kuma na ɗauke ta da matukar muhimmanci.
"Ina cikin matukar farin ciki a halin yanzu, Allah ke bada rayuwa kuma shi kaɗai ne ke ɗaukar ran mutum."

Read also

Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa

"Kuma Allah da kansa yace, idan na baka wani mulki to na baka wata dama ce a rayuwa; ni kadai zan iya kwace wa daga hannunka idan baka yi abinda ya dace ba."

Ina cikin koshin lafiya - Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Legas ya ƙara da cewa Allah ne ya raya kowa har ya kawo zuwa lokacin da yake tsaye a gaban masoya.

"Allah ne ya raya mu zuwa yau har ga shi ina tsaye a gabanku cikin koshin lafiya. Yau rana ce ta farin ciki da zamu mika godiya ga Allah."
"Ina muku addu'ar Allah ya saka muku da alkairi duk waɗanda suka zo wurin nan, naji daɗi sosai ba abinda zan ce sai godiya gareku."

A wani labarin mai kama da wannan kuma Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shine abin damuwa ba.

Read also

Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan

Atiku yace babu wani abu shugaban ƙasa daga kudu ko daga arewa, abinda duniya ta sani shine shugaban Najeriya.

Source: Legit.ng

Online view pixel