Kotu ta tsige shugabannin kananan hukumomi 16 na APC da gwamna ya naɗa a wannan jihar

Kotu ta tsige shugabannin kananan hukumomi 16 na APC da gwamna ya naɗa a wannan jihar

  • Babbar kotu ta yanke hukuncin rushe shugabannin riko da gwamnan Kwara ya naɗa a kananan hukumomi 16 na jihar
  • Kotun tace babu dalilin da zai sa gwamna ya rushe zababbun ciyamomi, kuma ya maye gurbinsu da kantomomi
  • Jam'iyyar adawa PDP ta bayyana jin daɗinta kan matakin kotun, inda tace wannan nasara ce ga mulkin demokaraɗiyya

Kwara - Babbar kotun jihar Kwara ta rushe kwamitin rikon kwarya da gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya naɗa domin su jagoranci kananan hukumomi 16 dake jihar.

Premium times ta ruwaito cewa gwamna AbdulRazaq ya naɗa shugabannin riko a ƙananan hukumomin jihar bayan dakatar da zababbu.

Amma a ranar Jumu'a, Mai shari'a Hassan Gegele, na babbar kotun jihar dake zama a Ilorin, ya bayyana matakin da gwamnan ya ɗauka da, "cin mutuncin mulki."

Kara karanta wannan

Bayan Goyon Bayan Gwamna APC, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Yuwuwar Wike Ya Fice PDP

Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq
Kotu ta rushe shugabannin kananan hukumomi da gwamna ya naɗa a wannan jihar Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gegele ya yi hukunci ne kan ƙarar da wata ƙungiyar al'umma ta shigar a gabansa, tana ƙalubalantar naɗa kwamitin riko da gwamnan jihar ya yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shin gwamnatin Kwara ta amince da hukuncin?

Da yake martani kan hukuncin kotun, Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a, Salman Jawondo yace gwamnati zata ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Tribune ta rahoto Jawondo yace:

"Muna tabbatar da cewa shari'a kan wannan lamarin ba ta kare ba, domin zamu ɗaukaka ƙara zuwa kotun Allah ya isa."

PDP ta ji daɗin wannan hukuncin

Da take bayyana ra'ayinta kan hukuncin, babbar jam'iyyar hamayya PDP ta yaba da hukuncin kotun.

A wata sanarwa da kakakin jam'iyyar PDP reshen jihar, Tunde Ashaolu, fitar ya bayyana hukuncin da kotun ta yanke da, "Cigaba mai kyau."

Hakazalika PDP ta yaba wa ƙungiyar ENetSuD bisa namijin kokarinta wajen yaƙi da karya doka da kuma neman adalci.

Kara karanta wannan

ISWAP Sun Fara Kafa Sansanoninsu a Yankunan Zamfara, Gwamnatin Jiha ta Koka

Sanarwar tace:

"Hukuncin kotun bai zo mana da mamaki ba, domin ya zo dai-dai da matsayar mu cewa gwamna ba shi da ƙarfin sallamar zaɓaɓɓun ciyamomi."
"Hukuncin da kotu ta yanke yau nasara ce ga mulkin demokaradiyya da kuma al'ummar jihar Kwara, waɗanda ke neman a musu adalci."

A wani labarin kuma Gwamna Umahi ya yi barazanar hukunta iyayen yan bindigan da suke tada yamutsi a jiharsa

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa ba zai sake amincewa wasu tsirarun mutane su cigaba da kashe mutane a jiharsa ba.

Umahi yace idan ya sake jin an tada zaune tsaye ko an kashe wasu, to zai kama iyaye, sarakuna da shugabannin yanki da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel