Alhaki: Mai garkuwa da mutane ya bindige abokin aikinsa yayin gumurzu da Jami’an tsaro

Alhaki: Mai garkuwa da mutane ya bindige abokin aikinsa yayin gumurzu da Jami’an tsaro

  • Jami’an Amotekun sun yi ram da wasu ‘yan bindiga da suka sace ‘dan kasuwa a Ondo
  • A kokarin kubuta daga hannun jami’an tsaron, wani ‘dan bindiga ya hallaka abokinsa
  • Wanda ya yi harbin ya tsere, amma an yi nasarar cafke daya daga cikin ‘Yan bindigan

Ondo - Wani mutumi mai suna Funmi Adenuoye da ake zargin mai garkuwa da mutane ya mutu a hannun daya daga cikin ‘yan gungun bindigansu a Ondo.

Jaridar Vanguard ta ce wani ‘dan bindiga ne ya harbe Funmi Adenuoye yayin da harbe-harbe ya kaure tsakanin ‘yan bindigan da dakarun tsaron Amotekun.

An bada sunan wanda ya harbe Adenuoye a matsayin Kunle. Rahoton yace Kunle ya kashe takwaransa yayin da suke kokarin tsere wa jami’an Amotekun.

Jami’an na Amotekun sun bi wadannan mutane ne bayan sun sace wani dillalin siminti mai suna Shakirudeen, ‘dan shekara 58 daga gidansa a jihar Ogun.

Read also

'Yan Gari sun tsokano Sojoji a Oguta, Jami’an tsaro sun tarwatsa fadar Sarki, an kashe mutane

A ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba, 2021, marigayin da abokan aikinsa biyu; Tayo Ibrahim da Kunle suka sace Alhaji Shakirudeen da nufin a biya su kudi.

Rahotanni sun ce wadannan mutane sun kawo ‘dan kasuwan garin Okitipupa a jihar Ondo, da nufin boye shi har sai lokacin da aka iya biyansu kudin fansa.

Jami’an tsaro
Sojojin Amotekun a Ondo Hoto: www.vanguardngr.com
Source: UGC

Dubun gungun ya cika

A nan ne rundunar Amotekun suka biyo su a sakamakon irin tukin ganganci da suka rika yi a hanya.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa Ibrahim mai shekara 28 ya fada hannun 'Yan Amotekun, ya kuma fallasa asirin sauran abokan aikin na sa.

Tayo Ibrahim yace har an yarda za a biya su Naira miliyan biyu domin su fito da dattijon da suka dauke, sai suka fada hannun jami’an tsaron sa-kai na Amotekun.

Read also

Jami’an DSS sun kama Hadimin Gwamna, mutum 2 da zargin satar kudin da aka ware wa talakawa

Kawo yanzu ana cigaba da tsare Ibrahim, Kunle wanda ya kashe takwaransa ya tsere .‘Yan bindigan sun harbi wani jami’in da yanzu yana jinya a asibiti.

Tauraron Nollywood ya fada hannun Sojoji

A ranar Alhamis ne aka samu labarin cewa Sojojin kasan Najeriya sun kama ‘Dan wasan kwaikwayo da yake goyon bayan kungiyar IPOB da aka haramta.

Da ake bada sanarwar, Janar Onyema Nwachukwu yace sojoji ba za su yarda a rika taimaka wa ‘yan ta’adda ba, ganin halin da ake fama da shi a kudu maso gabas.

Source: Legit

Online view pixel