'Yan Gari sun tsokano Sojoji a Oguta, Jami’an tsaro sun tarwatsa fadar Sarki, an kashe mutane

'Yan Gari sun tsokano Sojoji a Oguta, Jami’an tsaro sun tarwatsa fadar Sarki, an kashe mutane

  • An hallaka mutane yayin da fusatattun sojoji suka shiga kauyen Oguta
  • Ana zargin sojoji sun kutsa fadar Sarki, sannan sun rusa gidajen mutane
  • Mutanen gari ne suka tsokano fada bayan sun kashe wasu jami’an sojoji

Imo - Akalla mutane uku aka rahoto cewa sun mutu, baya ga gidaje 15 da aka ruguza a kauyen Aborshi Izombe da ke karamar hukumar Oguta, jihar Imo.

Daily Trust tace an shiga har fadar Mai martaba Sarkin Aborshi Izombe a ranar Juma’a. Mazauna garin sun ce sojojin kasa ne suka jawo aka kai hare-haren.

Majiyar ta ce an bata wa sojojin rai a sakamakon hallaka wasu jami’ai biyu da matasan Izombe suka yi.

Matasa sun yi zanga-zanga bayan kashe wani Chukwunoso Iherue. Ana zargin sojoji ne suka kashe shi, a dalilin haka ‘yan gari suka hallaka wasu sojoji biyu.

Read also

Yan sakai sun hallaka limamin masallaci da wasu mutum 10 a jihar Sokoto

A wani kaulin, rikici ya shiga tsakanin jami’an tsaro da mutanen garin ne saboda satar rigimar mai. Mutanen gari da sojoji duk suna satar danyen mai a yankin.

Sojan Kasa
Jami'in Sojan Najeriya Hoto: twentytendaily.com
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda abin ya auku

“Sojoji sun kashe wani Chukwunoso Iherue kafin matasa su maida martani, sai sojoji suka zo fadar Sarkin Aborshi Izombe, inda mutane suka kai masu hari.”
“Rahoton da muke samu shi ne sojoji sun kona fadar mai martaba Sarki Eze Muforo da wasu gidaje biyu a Umuokwu Izombe.”
“Sojojin sun kawo hari a motocin Hilux 18 dauke da gangunan fetur da motocin yaki. Wani ‘danuwana ya fada mani sun kona gidansu.”
“Bayan nan sojoji sun je sun kona gidajen Cif C A Onyeukwu kurmus.”

Da jaridar ta tuntubi rundunar 34 Artillery Brigade, Kyaftin Joseph Akubo ya bayyana cewa bai samu labarin abin da ya faru ba, ya yi alkawarin zai yi jawabi.

Read also

Alhaki: Mai garkuwa da mutane ya bindige abokin aikinsa yayin gumurzu da Jami’an tsaro

Mai garkuwa da mutane ya bindige abokinsa

Dazu aka ji cewa dakarun Amotekun sun rutsa masu satar mutan a Ondo, har wani ‘dan bindiga ya kashe takwaransa, aka kuma kashe wani jami'in Amotekun.

Gungun ‘Yan bindigan sun sace ‘dan kasuwa a jihar Ogun, suna neman a biya N2m. A kokarin kubuta ne wani ‘dan bindiga ya hallaka abokinsa har barzahu.

Source: Legit

Online view pixel