Tauraron Nollywood ya shiga hannun Sojoji, ana zarginsa da ba ‘Yan ta’adda goyon baya
- Dakarun sojojin kasa sun bayyana dalilin da ya sa suka cafke Chiwetalu Agu
- Mai magana da yawun sojoji yace ‘Dan wasan yana goyon bayan ‘Yan IPOB
- Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a jiya
Anambra - Dakarun sojojin kasar Najeriya sun ce sun kama ‘dan wasan kwaikwayon Nollywood, Chiwetalu Agu, bisa zargin nema wa kungiyar IPOB goyon-baya.
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana wannan a wani dogon jawabi da ta fitar a Facebook ta bakin mai magana da yawun sojojin kasa, Onyema Nwachukwu.
Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu yace an yi ram da Chiwetalu Agu ne a lokacin da yake tunzura jama’a. Amma ya musanya cewa sun galabaitar da Agu.
“Dakarun sojojin kasa (NA) sun kama wani Chiwetalu Agu a lokacin da yake kokarin tunzura al’umma, yana nema wa haramtaciyyar kungiyar IPOB goyon-baya.”
“Chiwetalu Agu ya yi irin shigar da aka san ‘yan kungiyar suna yi. An yi gaba da shi domin ayi masa tambayoyi a lokacin da yake zuga mutane su shiga kungiyar.”
“Duk da cewa ya yi yunkurin yin taurin-kai, dakarun sojoji sun tafi da shi a hannunsu, amma ba a galaibatar da shi ba, sannan bai fuskanci wata gallaza wa ba.”
A jawabin, sojojin Najeriya sun ce sun san kowa yana da hakki a matsayin shi na ‘dan kasa, amma ba a amince mutum ya yi abin da zai jawo rashin zaman lafiya ba.
Da yake bayani a madadin dakarun sojojin a Facebook, Janar Nwachukwu ya zargi Agu da yin abin da zai jawo rashin tsaro, yace sam ba za su yarda da wannan ba.
“Domin gudun kokwanto, har yanzu IPOB tana nan a matsayin kungiyar da aka haramta. Saboda kokarin tallata wannan kungiya, ya ci karo da dokar Najeriya.”
“Abin da ya fi tada hankali shi ne ganin halin da ake ciki a yankin, da kuma shirin da ake yi na Operation Dawn, aikinsa zai iya zama goyon bayan 'yan kungiyar.”
Daily Trust tace labarin kama wannan tauraron na Nollywood ya jawo surutai a shafukan sada zumunta.
Asali: Legit.ng