Rashin tsaro: Boko Haram sun karbe kauyuka 500 a Neja, suna raba wa mutane makamai

Rashin tsaro: Boko Haram sun karbe kauyuka 500 a Neja, suna raba wa mutane makamai

Shugaban karamar hukumar Shiroro yace ‘Yan Boko Haram sun shiga kauyuka

Sulaiman Chikuba ya roki Gwamnatin Tarayya ta kawo wa yankin Shiroro agaji

Hon. Chikuba yake cewa Boko Haram su na raba wa mutanen kauyuka makamai

NigerThis Day tace kungiyar Boko Haram ta karbe kauyuka sama da 500 a wasu mazabu da ke karamar hukumar Shiroro, jihar Neja.

A daidai wannan lokaci ne kuma ake samun labari cewa an hallaka mutane 10 a kauyen Munya da ke makwabtaka da garin na Shiroro.

Shugaban karamar hukumar Shiroro, Sulaiman Chikuba, ya tabbatar da harin da ‘yan bindiga suka kai a ranar Alhamis da ta gabata.

Maganar da Hon. Sulaiman Chikuba ya yi, ya zo daidai da abin da James Isaac Jagaba ya shaida wa manema labarai jiya a garin Minna.

Read also

Kano: Matashi mai shekaru 21 ya jagoranci fashi a gidan maƙwabcinsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu garuruwan Boko Haram suka shiga?

An rahoto Chikuba yana cewa gundumomin da ‘yan ta’addan suka karbe sun hada da; Manta, Gurmana, Bassa-Kokki da kuma Allawa.

Haka zalika an karbe Kurebe, Kushaka, Kwati, da Chukumba, har ta kai ‘yan Boko Haram suna kokarin jan ra’ayin mazauna yankin.

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya Hoto: guardian.ng
Source: UGC

‘Yan ta’addan Boko Haram suna ba mazauna makamai da nufin su yaki jami’an tsaro da gwamnati.

Ana ba mazauna kayan fada

“A matsayina na shugaban karamar hukumar Shiroron jihar Neja, ina iya fada maku cewa baya ga matsalar ‘yan bindiga, Shiroro tana fama da matsalar Boko Haram. Ina da hujja a kan wannan.”
“Boko Haram sun ce ba su son karatun firamare da sakandare, makarantar addini kurum suke so.”
“Suna kokarin jawo mazauna cikin kungiyarsu, su na ba su makamai domin su taimaka masu wajen yakar gwamnati.”

Read also

A shirye nake na taimakawa kasar Sudan don ta ci gaba, inji shugaba Buhari

A karshe shugaban karamar hukumar ya roki gwamnatin tarayya ta karo jami’an tsaro domin su yaki ‘yan Boko Haram da suka tare a garin na Shiroro.

Kwatan Daban Masara: DHQ tayi magana

A makon nan ne hedikwatar tsaro ta bayyana abin da ya faru a harin Kwatan Daban Masara inda luguden Sojin sama ya hallaka mutanen da ke kamun kifi.

Kakakin DHQ yace binciken da tayi ya nuna wa Sojojin cewa mayakan ISWAP suna boye a yankin Arewa maso gabas, sun fake wa da kiwon kifi, suna ta'adi.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel