Kano: Matashi mai shekaru 21 ya jagoranci fashi a gidan maƙwabcinsa

Kano: Matashi mai shekaru 21 ya jagoranci fashi a gidan maƙwabcinsa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama Abdullahi Musa, matashi mai shekaru 21 bisa zargin sa da fashi da makami
  • Ana zargin Musa da jagorantar fashi wurin kai wa makwabcin sa farmaki a Yanadawa Quarters da ke jihar Kano
  • Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Talata, 5 ga watan Oktoba

Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama Abdullahi Musa, mai shekaru 21 bisa jagorantar fashin gidan makwabcin sa da ke Yamadawa Quarters a cikin Kano, kamar yadda LIB ta ruwaito,

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Talata, 5 ga watan Oktoba inda ya ce Musa da sauran mutane biyu da su ka hada kai wurin ta’addancin su na cikin mutane 51 da su ka addabi jihar yanzu haka da fashi da makamai har da sayar da miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

Kano: Matashi mai shekaru 21 ya jagoranci fashi a gidan maƙwabcinsa
Matashi mai shekaru 21 ya jagoranci fashi a gidan maƙwabcinsa a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kamar yadda Kiyawa ya bayyana, Musa ya tabbatar da cewa shi ne ya jagoranci fashin sannan ya raka jami’an tsaro don su kama sauran mutane 2 da suka hada kai wurin fashin.

Har datsar maƙwabcin su ka yi da wuka

Bisa ruwayar LIB, Kiyawa ya bayyana cewa:

“A ranar 12 ga watan Afirilun 2021 da misalin karfe 5 na safe, mun samu rahoto daga wani mazaunin Janbulo Yamadawa Quarters dake Kano, cewa ‘yan fashi 4 sun shiga har gidan sa ta katanga inda su ka balle kofar dakin sa suka datsi matar sa sannan su ka datse shi a hannu da wuka.”
“Sun kuma tsere da na’ura mai kwakwalwa guda 2, Nova 4, Nlate 9, wayoyi 2 kirar Huawei, Tabijin din bango, flash guda 2 da sauran kaya har da kudi N100,000.

Kara karanta wannan

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

“Bayan faruwar lamarin ne a ka yi gaggawar wucewa da shi asibitin kwararru na Murtala dake Kano inda aka kwantar da shi sannan kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya umarci rundunar ‘yan sanda ta kamo wadanda ake zargin bisa jagorancin SP Bashir Musa Gwadabe. Take anan rundunar ta fara aikin ta.
“Bayan kama ‘yan fashi kuma masu sayar da miyagun kwayoyin guda 51, sai aka gano cewa daya daga cikin su, Abdullahi Musa mai shekaru 21 adireshin su daya da wanda lamarin ya faru dashi.
“Bayan kammala bincike, wanda ake zargin ya bayyana cewa shi ya jagoranci ‘yan fashin."

Bayan bincike mai zurfi, Garba Moh’d, daya daga cikin ‘yan fashin ya bayyana yadda ya tura wayoyi wurin 100 zuwa kasar Nijar.

“Har ila yau, wani Musa Sunusi ya bayyana yadda ya siya wayoyi 9 daga hannun ‘yan fashin. Duk wadanda ake zargin sun amsa laifukan su kuma za a yanke mu su hukunci da zarar an kammala bincike.”

Kara karanta wannan

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi

A wani labarin daban, kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.

An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.

King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164