A shirye nake na taimakawa kasar Sudan don ta ci gaba, inji shugaba Buhari

A shirye nake na taimakawa kasar Sudan don ta ci gaba, inji shugaba Buhari

  • Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, a shirye gwamnatinsa take don taimakawa Sudan ta kudu
  • Ya bayyana haka ne yayin da ya ke gabatar da jawabi a taron rantsar shugaban kasar Habasha a yau Talata
  • Shugaba Buhari ya bayyana cewa, akwai bukatar aiki tukuru don wanzar da zaman lafiya a yankunan Afrika

Habasha - Rahoto daga jaridar Punch ya ce, shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya ce a ko da yaushe Najeriya a shirye take ta ba Jamhuriyar Sudan ta Kudu taimako don samun kwanciyar hankali na siyasa da tattalin arziki.

Ya bayyana haka ne yayin da yake nuna damuwarsa game da rashin kwanciyar hankali na siyasa a Libya, yana mai cewa muddin kasar ba ta da kwanciyar hankali, yaduwar makamai da manyan makamai a yankin Sahel zai ci gaba.

Kara karanta wannan

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

Buhari ya ce kasar Sudan ta tambayi ko meye take so zai taimake ta
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Buhari ya fadi haka ne a ranar Talata 5 ga watan Oktoba a Addis Ababa yayin ganawar bangarorin biyu da Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu, inji PM News.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken ‘Ko da yaushe za mu iya mika taimako ga Sudan ta Kudu, in ji Shugaba Buhari’.

Shugaban wanda ya ba da tabbacin cikakken goyon bayan Najeriya ga duk kokarin kawo kwanciyar hankali da wadata na dogon lokaci a Nahiyar ya ce:

‘’Najeriya za ta ba da gudummawar ta yadda ya kamata don ci gaban Sudan ta Kudu. Ku sanya kwarin giwarku a kanmu ku tambaye mu abin da za mu iya yi.”

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Da yake jaddada bukatar hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa, Buhari ya ce tare da saka hannun jari a ilimi, inganta tattalin arziki, da kiwon lafiya, tabbas abubuwa za su inganta.

Dangane da halin da ake ciki a Guinea da Mali, ya sake nanata cewa dole ne shugabannin Afirka su goyi bayan kokarin da aka yi don dawo da mulkin dimokuradiyya a kasashen.

Martanin shugaban Sudan ta kudu

A nasa jawabin, Shugaba Kirr, wanda ya amince da rawar da Najeriya ke takawa a Afirka, ya yaba da kokarin da kasar ke yi a fafutukar kwato 'yancin Sudan ta Kudu.

Ya kuma yabawa Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, kan yadda ta taimaka wajen ilmantar da ‘yan matan Sudan ta Kudu da dama a kasar.

A cewarsa:

‘’A Yammacin Afirka, ECOWAS na shiga tsakani a duk lokacin da wata kasa ta samu matsala. Ya kamata a ke hakan a Gabas da Tsakiyar Afirka."

Kara karanta wannan

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

Shugaba Buhari da Shugaba Kirr na daga cikin shugabannin Afirka da dama da suka halarci bikin rantsar da Firayim Minista Abiy Ahmed na Habasha na wa'adin mulki na shekaru biyar karo na biyu.

Sauya sheka: Gwamna Buni ya karbi mambobin majalisar jihar Anambra 11 zuwa APC

A baya mun kawo cewa, Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin tsare-tsaren babban taron jam'iyyar APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni ya karbi wasu jiga-jigan siyasar jihar Anambra daga wasu jam'iyyu zuwa APC.

Ana ci gaba da yawaita sauya sheka a cikin wannan shekara, lamarin da ya kawo cece-kuce a jam'iyyun siyasa daban-daban na Najeriya.

Cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gwamna Buni ya fitar a shafinsa na Facebook, mun samu cikakken bayani kan karbar wadannan sabbin shiga ga jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.