Kotu ta yankewa Femi Adesinan bogi dauri mai tsauri, zai yi shekaru 28 a gidan kurkuku

Kotu ta yankewa Femi Adesinan bogi dauri mai tsauri, zai yi shekaru 28 a gidan kurkuku

  • An kammala shari’a da wani da ya damfari Bayin Allah da sunan Femi Adesina
  • Hukumar EFCC tayi nasarar jefa Jamiu Isiaka na tsawon shekaru 28 a kurkuku
  • Kotu ta karbe gidaje da wasu dukiyoyin Jamiu Isiaka bayan an same shi da laifi

Kwara - Alkali Mahmud Abdulgafar na babban kotun jihar Kwara da ke zama a Ilorin, ya yanke hukunci a kan wani da ya yi karya da sunan Femi Adesina.

Wannan malamin addini mai suna Jamiu Isiaka da ya rika karya da sunan hadimin shugaban Najeriyar, zai shafe shekaru 28 yana zaman kaso a kurkuku.

Tribune tace Mahmud Abdulgafar ya samu Jamiu Isiaka da laifin sata ta hanyar amfani da sunan wasu.

Alkali ya zartar da hukunci cewa laifuffukan da Isiaka ya aikata, sun saba wa sashe na 1(1) (a) na dokar sata da sauran makamantan laifuffuka na shekarar 2006.

Read also

An yi jana'izar mahaifin kakakin majalisar Zamfara da ya rasu a hannun 'yan bindiga

Kotu tace wannan mutumi da aka samu da laifin sata da damfara, zai zauna a gidan gyaran hali na Mandala da ke Ilorin, jihar Kwara har na tsawon shekaru 28.

Mahmud Abdulgafar ya bayyana cewa lauyoyin da suka gurfanar da Isiaka sun iya tabbatar da cewa ya aikata laifuffukan da hukumar EFCC ke zarginsa da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Femi Adesinan bogi
EFCC ta kama Jamiu Isiaka Hoto: officialefcc
Source: Facebook

Isiaka ya yi karyar shi ne mai magana da yawun shugaban Najeriya, Femi Adesina da kuma tsohon shugaban NNPC, Maikanti Baru domin ya damfari wani.

A haka ne Isiaka ya karbi Naira miliyan 30 a hannun wani mutumin kasar Koriya, Keun Sig Kim.

Jaridar tace EFCC tace matashin mai shekara 33 ya fake da sunan manyan gwamnati, ya damfari mutanen kasar waje da sunan zai sama masu lasisin shigo da mai.

Read also

VAT: Gwamnonin Arewa za su hada-kai da Gwamnatin Tarayya suyi shari’a da Jihohin Kudu

Lauyan da ya tsaya wa hukumar EFCC, O. B Akinsola ya kira wasu shaidu biyu da suka fada wa kotu yadda Isiaka ya rika karbar kudin mutane ta hanyar damfara.

Baya ga zaman kurkuku an karbe gidan Isiaka a Oke-Foma a Ilorin, da motarsa kirar Toyota Corolla, da talabijin da na’urorin AC, na wanki da na ajiye ruwan sanyi.

Buhari zai yi magana gobe

Shugaban kasa zai yi jawabin murnar samun ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba, 2021. Idan za ku tuna, Femi Adesina ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar.

Muhammadu Buhari zai yi wa mutanen Najeriya jawabi da karfe 7:00 na safe a gidajen talabijin da rediyo.

Source: Legit

Online view pixel