'Batanci: Kotun Shari'a a Kano ta ƙi bada belin Sheikh Abduljabbar

'Batanci: Kotun Shari'a a Kano ta ƙi bada belin Sheikh Abduljabbar

  • Kotun shari'a na jihar Kano ta hana Malamin mazaunin Kano Sheikh Abduljabbar Kabara beli
  • Sabbin lauyoyinsa sun nemi a bada belinsa ne don iyalansa sun shiga mawuyancin hali
  • Amma kotun karkashin jagorancin Ibrahim Sarki Yola ta hana belin tana mai cewa babu kwakwaran dalilin da za a bashi belin

Jihar Kano - Babban kotun shari'a da ke zamanta a jihar Kano ta ki amincewa da bukatar beli da malamin Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar, Daily Trust ta ruwaito.

Ana zargin Abduljabbar Kabara ne da laifin batanci da tunzura da tada zaune tsaye.

'Batanci: Kotun Shari'a a Kano ta ƙi bada belin Sheikh Abduljabbar
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

A zaman kotun na ranar Alhamis, sabbin lauyoyi masu kare Kabara, karkashin jagorancin Muhammadu Umar, sun nemi a bada shi beli kan cewa iyalansa sun shiga mawuyacin hali saboda rashinsa.

Read also

Tsohon Sarki Sanusi ya soki tsarin biyan tallafin fetur, ya fallasa badakalar da ke cikin tsarin

Lauyoyi masu kare wanda ake tuhuma sun ce idan an bashi belin zai samu lokaci na kare kansa yadda ya kamata.

Lauyoyi masu shigar da kara, karkashin jagorancin Suraj Saida (SAN), sun ki amincewa da bukatar neman belin da wanda ake zargin ya shigar, inda suka ce bai hallata a bada beli ga wanda ya aikata babban laifi da ya cancanci kisa ba sai dai a yanayi na musamman.

Alkalin kotun, Ibrahim Sarki Yola, ya yanke hukuncin cewa babu wani abu na musamman da za ta saka kotun ta bawa wanda ake zargin beli don haka ta bada umurnin a cigaba da tsare shi a gidan gyaran hali.

Kotun ta kuma dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Oktoban shekarar 2021.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel