Tsohon Sarki Sanusi ya soki tsarin biyan tallafin fetur, ya fallasa badakalar da ke cikin tsarin
- Muhammadu Sanusi yace wasu manya ne suke cin moriyar tsarin tallafin fetur
- Tsohon Sarkin Kano yana ganin ba arahar man fetur al'umma suka fi bukata ba
- Sanusi yace saboda manya na amfana da tsarin ne har yau aka ki dakatar da shi
Abuja - Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, yace kudin da gwamnatin tarayya take biya da sunan tallafin man fetur, salon sata ne kurum.
The Cable ta kawo rahoto inda aka ji tsohon sarkin yana sukar wannan tsari da ya yi sanadiyyar da gwamnatin tarayya ta rasa N714bn cikin watanni bakwai.
Muhammadu Sanusi ya yi magana da gidan talabijin na Arise TV, inda yace gwamnatocin da aka yi sun cigaba da biyan tallafin mai duk da illar wannan tsari.
Sanusi wanda ya yi gwamnan babban banki tsakanin 2009 da 2014 yace kuskuren da ake yi da farko shi ne gwamnati ta dauka Najeriya kasa ce mai arzikin mai.
A ra’ayin Sanusi II, babbar bukatar mutanen Najeriya ba arahar man fetur bane, a lokacin da ake fama da karancin asibitoci, wutar lantarki da kuma hanyoyi.
Najeriya ba ta da arziki irin kasar Saudi
“Mun yi ta yin kura-kurai, kuma shi ne ya jawo wa gwamnatocin da ake ta yi kuskure. Kuskuren farko shi ne daukar Najeriya da ake yi kasa mai arzikin mai.”
“Na tuna 2011, a lokacin da muke maganar tallafin fetur da Jonathan ya so ya soke tsarin.”
“Najeriya tana tace ganguna miliyan biyu ga mutane miliyan 160; mutum 80 suna raba kowace ganga. Saudi tana samar da ganga daya ga mutanenta uku.”
A karshe Sanusi yace ana cinye duk kudin da aka samu daga arzikin mai, sai ya zama mutum 160 suke raba kowace gangar mai, akasin abin da ake gani a Saudi.
Masu uwa a gindin murhu suna amfana?
“Abin da ya sa aka cigaba shi ne akwai wasu a kusa da madafan iko da suke samun biliyoyin daloli da wannan tallafin. Ba don haka ba, da an daina.”
“Muna da wannan tsari da ake kira tallafin man fetur wanda ainihi badakala ce, duk abin da aka samu, yana tafiya – A shigo da mai, a biya tallafinsa.”
Buhari ya yi wa jama'a jawabi
A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka ji shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa mutanen Najeriya jawabi domin taya su murnar bikin samun 'yancin kai.
Shugaban kasar ya tabo batun tsaro, Twitter, tattali, tsadar abinci da N-Power a jawabinsa, yace akwai wani ‘Dan Majalisa cikin masu ba ‘Yan ta’adda goyon-baya.
Asali: Legit.ng