Osinbajo: Mun tsare kasuwancin mutane miliyan 1 daga hadari a lokacin annobar COVID-19

Osinbajo: Mun tsare kasuwancin mutane miliyan 1 daga hadari a lokacin annobar COVID-19

  • Yemi Osinbajo ya bayyana yadda gwamnatinsu ta tsare tattalin arzikin Najeriya
  • Mataimakin shugaban kasa yace kasuwanci sun tsira duk da annobar COVID-19
  • Farfesa Osinbajo yake cewa gwamnatin tarayyar ta hana kasuwanci tashi a aiki

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, yace tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnatin nan sun ceci sana’ar mutane miliyan daya daga durkushe wa.

Punch tace Farfesa Yemi Osinbajo yake cewa tsare-tsaren sun hana a rufe kananan kasuwanci 150, 000 a lokacin da annobar cutar COVID-19 ta addabi kasashe.

Mataimakin shugaban kasar yace shirye-shiryen gwamnatin Muhammadu Buhari sun yi maganin talauci, suka samar da ayyukan yi, suka inganta rayuwa.

Farfesa Osinbajo ya yi wannan bayani a ranar Talata, 28 ga watan Satumba, 2021, wajen wani zama da majalisar dinkin Duniya ta shirya ta kafar yanar gizo.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka bankado yunkurin ISWAP na kai wa tubabbun Boko Haram farmaki

Laolu Akande ya fitar da jawabin da mataimakin shugaban Najeriyar ya gabatar a birnin Abuja.

Yemi Osinbajo ya gabatar da jawabi mai taken ‘Why social protection schemes are crucial’ domin ya yi bayanin fa’idar manufofin da gwamnatin APC ta kirkiro.

Osinbajo da Buhari
Shugaba Buhari da Mataimakinsa, Farfesa Osinbajo Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewar Osinbajo, tsarin ESP ya taimaka wajen rage radadin tattalin arziki, magance kalubalen kiwon lafiya, samar da ayyuka, da kuma ceton marasa karfi.

Jaridar ta rahoto Akande yana cewa tsarin tattalin arzikin ya kunshi aikin kiwon lafiya, harkar hona, gina gidaje, samar da wuta da abubuwan more rayuwa.

“Mun tsare sana’o’i miliyan daya, mun hana kananan kasuwanci 150, 000 tashi aiki. Mun kuma taimaka wa marasa karfi da tsare-tsaren tattalinmu.”
Tsare-tsarenmu sun taimaka wajen cigaba da tura kudin gaggawa ga talakawan da ke birni.”

Kara karanta wannan

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana yadda suka tsare tattalin arzikin Najeriya. Mataimakin shugaban kasa yace kasuwanci sun tsira duk da annobar COVID-19.

Dole 'Dan takarar 2023 ya san tattalin arziki

A makon nan ne Yaron Abubakar Tafawa Balewa, Billy ya caccaki ‘Yan siyasar Kudancin Najeriya da suke cewa dole ne mulki ya koma hannunsu a zabe mai zuwa.

Abubakar Tafawa Balewa yana da ra'ayin cewa duk ‘Dan takarar da ya iya allonsa ya wanke a 2023, ko Bahaushe ne ko Bayarabe, muddin ya fahimci tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel