Kyautar motar N200m da aka ba Sarki Aminu Ado Bayero na iya jefa shi a hadari inji Kungiya

Kyautar motar N200m da aka ba Sarki Aminu Ado Bayero na iya jefa shi a hadari inji Kungiya

  • Defenders of Arewa Heritage ta soki tallata kyautar da aka yi wa Sarkin Kano
  • Kowa ya ji labari Abdul Samad Rabiu ya ba Aminu Bayero Rolls Royce Phantom
  • Kungiyar tace bai kamata a rika yamadidi da kyautar da aka ba Mai martaba ba

Kano – Surutan da ake yi a kan kyautar motar da aka ba Sarkin Kano bai dace ba. Wannan ne ra’ayin wata kungiya mai suna, Defenders of Arewa Heritage.

Kungiyar Defenders of Arewa Heritage tace bai kamata labarin kyautar motar alfarma ta Rolls Royce da aka ba Mai martaba Aminu Ado Bayero ya fita fili ba.

Wannan kungiya tana magana ne kan kyautar Rolls Royce Phantom da Attajirin Kano, shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ba Aminu Ado Bayero.

Shugaban Defenders of Arewa Heritage, Idrissa Mala da jami’in sadarwa na kungiyar, Hakeem Raji sun fitar da jawabi na musamman a kan batun a ranar Talata.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Laifi ne a ba Sarki kyauta?

“Babu laifi don Attajirin ‘dan kasuwa ya bada kyautar mota.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarki Aminu Ado Bayero
Alhaji Aminu Ado Bayero Hoto: pmnewsnigeria.com
Source: UGC

“Matsalar kurum ita ce yadda aka rika tallata kyautar. Masu mulki na samun kyautttuka na alfarma daga abokansu da jami’an gwamnati a ko ina a kasar nan.”
“A Borno misali irinsu Muhammed Indimi, marigayi Ahmed Mai Deribe, da Bukar Mandara duk sun taba ba Shehun Borno mota. Amma ba a taba yada wa ba.”

Wannan kungiya tace an ba tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kyautar motar Rolls Royce Phantom har biyu a lokacin da yake kan karagar mulki.

“Babu wanda ya san cewa aminan Sarki Sanusi II; Kola Kareem and Hajiya Bola Shagaya ne suka ba shi kyautar motocin.”
“Sanusi II ya bayyana sunayensu ne a lokacin da aka zarge shi da kashe kudin masarauta wajen sayen motocin alfarma.”

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Kungiyar take cewa a matsayin musulmai, babu dalilin a tallata kyauta. Baya ga wannan, yin hakan zai iya jawo ‘yan bindiga su fara harin sabuwar motar Sarkin.

An kai Sarki kara a Ogun

A makon nan aka ji labari cewa Gimbiyar Sarkin Orile-Kemta, Halima Oniru ta shigar da karar Mai Martaba a gaban ‘Yan Sanda, tace ya cinye mata miliyoyin kudi.

Halima Oniru tace Mai martaban yayi ta karbe mata kudi, da suka yi aure ta gane ‘dan damfara ta aura.

Source: Legit.ng

Online view pixel