Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da AVM Sikiru Smith (rtd) a jihar Legas

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da AVM Sikiru Smith (rtd) a jihar Legas

  • Yan bindgia sun bulla a jihar Legas
  • An yi awon gana da 'dan uwan tsohon Sifeto Janar na yan sanda
  • Yan sanda sun lashi takobin ceto tsohon Sjan

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da Air Vice Marshal Sikiru Smith (retd.), a unguwar Ajah dake jihar Legas, rahoton Punch.

Wanda aka sace tsohon babban Soja ne kuma dan'uwa ga shugaban hukumar jin dadin yan sanda, Musuliu Smith.

An tattaro cewa yan bindigan sun saceshi ne yayinda yake wajen duba aikin da kamfaninsa Double Wealth Ventures Limited ke yi a Ajah.

Bayan harbe-harben bindiga, yan bindigan suka shige jirgin ruwa sukayi gaba da shi.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da AVM Sikiru Smith (rtd) a jihar Legas
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da AVM Sikiru Smith (rtd) a jihar Legas
Source: Facebook

Read also

Ba mu ci ta zama ba: 'Yan sanda sun dukufa a aikin ceto wani babban soja da aka sace

A cewar jawabin direbansa, Kofur Odiji, sai da tsohon Sojan ya fafata da yan bindigan kafin suka samu nasarar tafiya da shi.

Odiji yace:

"Suna na Kofur Odiji, dogari ga AVM Smith. An yi awon gaba da shi a inda muke aiki yanzun nan. Wasu yan bindiga masu fuskoki a rufe sun sace Oga yanzu."
"Yayinda na gabato na gansu suna tafiya da shi cikin jirgin ruwa babu bindiga hannuna."

Yan sanda sun dukufa a aikin ceto wani babban soja da aka sace

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a ranar Talata 28 ga watan Satumba ta ce bata ci ta zama, kuma ta tura dukkan zakakuran jami'anta don ganin an ceto AVM Sikiru Smith mai ritaya daga hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da shi.

Mai magana da yawun rundunar sandan jihar, CSP Adekunle Ajisebutu, shine ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan sace babban hafsan na sojin sama.

Source: Legit

Online view pixel