Ba mu ci ta zama ba: 'Yan sanda sun dukufa a aikin ceto wani babban soja da aka sace

Ba mu ci ta zama ba: 'Yan sanda sun dukufa a aikin ceto wani babban soja da aka sace

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta bayyana cewa, tana kan aikin ceto wani jami'in soja da aka sace
  • A jiya ne aka sace wani tsohon jami'in sojin saman Najeriya yayin da yake aiki a wani wuri
  • Rahotanni sun bayyana cewa, direbansa ne ya sanar da hukumomi yadda lamarin ya faru suna tare

Legas - Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a ranar Talata 28 ga watan Satumba ta ce bata ci ta zama, kuma ta tura dukkan zakakuran jami'anta don ganin an ceto AVM Sikiru Smith mai ritaya daga hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da shi.

Mai magana da yawun rundunar sandan jihar, CSP Adekunle Ajisebutu, shine ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan sace babban hafsan na sojin sama, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Rahoto ya nakalto shi yana cewa:

"Muna kan aiki don ceto shi."
An sace babba: Muna aiki don ceto AVM Smith, in ji 'yan sandan jihar Legas
AVM Sikiru Smith | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya fitar da rahoton cewa wasu 'yan bindiga da abin rufe fuska sun afka wa wani wurin aiki, inda suka sace jami'in rundunar sojin saman da ya yi ritaya a daren Litinin 27 ga watan Satumba a kan hanyar Ajah-Badore, jihar Legas.

A cikin wani sautin SOS da direban sa, Cpl. Odichi ya sake, ya ce an sace mai gidan nasa ne daga wani wurin aiki da ke Ajah sannan aka cilla da shi da karfi a cikin jirgin ruwa zuwa yankin Ikorodu na jihar.

A cikin sautin na minti daya da dakika hudu, Odichi ya ce:

“Barka da maraice. Don Allah, wannan batu ne na gaggawa. Ni ne Corporal Odichi, ina tare da AVM Smith. An sace Oga yanzun nan daga wurin da muke aiki. Wasu 'yan bindiga sanye da abin rufe fuska yanzu sun zo, sun fita da shi daga wurin."

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Yan bindiga sun yi awon gaba da AVM Sikiru Smith (rtd) a jihar Legas

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da Air Vice Marshal Sikiru Smith (retd.), a unguwar Ajah dake jihar Legas, rahoton Punch.

Wanda aka sace tsohon babban Soja ne kuma dan'uwa ga shugaban hukumar jin dadin yan sanda, Musuliu Smith.

An tattaro cewa yan bindigan sun saceshi ne yayinda yake wajen duba aikin da kamfaninsa Double Wealth Ventures Limited ke yi a Ajah.

Bayan harbe-harben bindiga, yan bindigan suka shige jirgin ruwa sukayi gaba da shi.

Manjo a soja ya maka rundunarsu da bankin FCMB a kotu kan daskarar da asusunsa

A wani labarin, wani Manjo a rundunar soji, Akeem Adeeogba Osenifor ya maka sojin Najeriya da bankin FCMB kan wasu kudade.

Manjon ya zargi rundunar soji da bankin da daskarar da asusun bankinsa tare da binciken gidansa ba tare da umurnin kotu ba, SaharaReporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

A cikin karar da ya shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, jami’in ya roki kotun da ta umarci wadanda ake kara su biya shi wasu makudan kudade da suka kai N16.6m a matsayin kudin da yake zargi an sace daga gidansa tare da wasu kadarori masu daraja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel