'Yan fashin daji da ISWAP a Sokoto: Sojin Najeriya sun yi rugu-rugu da 'yan ta'adda, Jami'ai

'Yan fashin daji da ISWAP a Sokoto: Sojin Najeriya sun yi rugu-rugu da 'yan ta'adda, Jami'ai

  • Sojojin rundunar Operation Hadarin Daji tare da wasu cibiyoyin tsaron sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP da 'yan fashin daji
  • Miyagun sun kai farmaki sansanin sojin ne yayin da wasu sojin suka tafi inda aka tura su ayyukan tsaron jama'a
  • Tuni kuwa dakarun suka ragargaji 'yan bindigan tare da bin wasu har kauyen Bassira da ke jamhuriya Nijar

Sokoto- Dakarun rundunar Operation Hadarin Daji, tare da hadin guiwar sauran hukumomin tsaro sun halaka miyagun 'yan ta'addan Islamic States for West African Province, ISWAP da 'yan bindiga a jihar Sokoto.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Benjamin Sawyer ya fitar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta wallafa.

Sojin Najeriya sun yi rugu-rugu da 'yan bindiga a Sokoto, Jami'ai
Sojin Najeriya sun yi rugu-rugu da 'yan bindiga a Sokoto, Jami'ai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce an sheke 'yan ta'addan yayin wani farmaki da suka kai Forward Operation Base, FOB, da ke Burkusuma, wata iyakar kauye da ke kusa da jamhuriyar Nijar a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

"Gagarumin aikin da dakarun FOB suka yi a cikin watanni da suka gabata a yankin arewa maso yamma ya tada hankulan mayakan 'yan ta'addan ISWAP da 'yan fashin daji."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Sawyer ya sanar da cewa maharan sun zo da yawansu yayin da suke amfani da layikan sadarwa na kasar da ke makwabtaka kuma sun manne a yankunan da babu tsaro sosai.

"Wannan ya faru ne yayin da dakarun suka fita domin ayyukan da aka tura su yankunan."

Ya bayyana cewa, dakarun sun sheke miyagun 'yan ta'addan masu tarin yawa yayin da suka yi arba.

"Sai dai kuma, a gaggawar da wasu dakarun suka yi wurin kai wa 'yan uwansu dauki, sun sheke 'yan ta'addan ISWAP masu tarin yawa, yayin da wasu suka tsere da miyagun raunika.
“Dakarun a halin yanzu sun fattaki miyagun 'yan ta'addan har zuwa Bassira da ke jamhuriyar Nijar," yace.

Kara karanta wannan

Sojojin Nijar sun ceci sojin Najeriya da 'yan bindiga suka kai wa farmaki sansaninsu a Sokoto

'Yan fashin daji sun koma hawa rakuma yayin da dokar siyan fetur a jarkoki ta tsananta

A wani labari na daban, 'yan fashin dajin da tsananin dokar hana siyan fetur a jarkoki ta dama a halin yanzu sun koma amfani da rakuma, kamar yadda majiyoyi suka sanar.

A cikin makon da ya gabata ne 'yan sanda suka dinga cafke jama'a da aka gano suna kai wa 'yan fashin dajin fetur a cikin dajika, Daily Trust ta ruwaito.

A kalla gwamnoni uku na yankin arewa maso yamma ne suka haramta siyar wa masu jarkoki man fetur domin dakile farmakin 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel