Gwamnatin Tarayya ta ba jami’an tsaro nan da 2022 a kawo karshen rashin tsaro a Najeriya
- Hon. Babajimi Benson yace an ba jami’an tsaro lokaci su kawo zaman lafiya
- ‘Dan Majalisar yake cewa ana sa ran nan da 2020 a ga karshen ‘Yan bindiga
- Hon. Benson ba ya goyon bayan a rika nema wa sojojin Boko Haram afuwa
Lagos - Gwamnatin tarayya ta bukaci rundunar sojoji da sauran jami’an tsaro su kawo karshen duk wata matsalar ta’addanci da ‘yan bindiga da ake fama da su.
Jaridar Vanguard tace shugaban kwamitin tsaro a majalisar wakilan tarayya, Babajimi Benson ya bayyana wannan a lokacin da ya gana da ‘yan jarida a Legas.
Honarabul Babajimi Benson ya halarci bikin yaye sojoji da suka yi kwas a makarantar Nigerian Armed Forces Resettlement Centre Trainees da ke garin Oshodi.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, ‘dan majalisar ya ba jami’an tsaron wa’adin nan da watan Maris na 2022, domin tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar nan.
Saboda a iya cin ma wannan burin, ‘dan majalisar kasar yace an biya duk wasu kudi da ake bukata domin sojoji su saye kayan aiki da manhajar da ake bukata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda za a samu zaman lafiya
Babajimi Benson yake cewa gidauniyar da za a kafa za ta taimaki sojojin wajen kawo zaman lafiya.
“An bada wa’adi zuwa Maris 2022 domin sojoji su kauda duk wasu masu tada kafar baya da ire-irensu. An biya kudi domin a saye kayan aiki da manhajoji.”
“Batun kafa gidauniyar tallafa wa sojoji, kudiri ne da na kawo, kuma yanzu ya tsallake mataki na uku a majalisa, za a amince da shi, sai a aika wa sanatoci.”
Da yake bayanin silar matsalar tsaro, Benson yace daukar dabbobi daga Arewa zuwa kudancin kasar shi ne babban abin da ya haddasa rigima a fadin kasar.
Ya dace ayi wa 'Yan Boko Haram afuwa?
A matsayinsu na shugabanni, Benson ya bukaci a fito da tsare-tsaren tattalin arziki da za su taimaki mutane, ya kuma nuna bai goyon bayan yi wa miyagu afuwa.
"Mutanen da suka tafka laifuffuka, bai kamata a yafe wa 'yan ta'adda ba, doka tayi aiki a kansu."
An fara yakin 2023?
An ji cewa Ministoci sun yi watsi da kungiyoyin da ke masu shisshigi, suna masu kamfe tun yanzu.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatude Fashola yace bai san da zaman masu cewa zai yi takara a 2023 tare da Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ba
Asali: Legit.ng