Masoya da aka yi garkuwa da su sun samu 'yanci ana jajiberin ɗaurin aurensu

Masoya da aka yi garkuwa da su sun samu 'yanci ana jajiberin ɗaurin aurensu

  • Allah ya ceci wasu masoya biyu da masu garkuwa da mutane suka sace su a hanyar siyo kayan bikin aurensu
  • An sako masoyan ne dai kwana daya kafin ranar daurin aurensu kamar yadda majiyoyi suka tabbatar
  • Kakakin 'yan sandan jihar Ekiti ya tabbatar da ceto su yana mai cewa 'yan sanda da sauran jami'an tsaro sun taimaka

Ekiti - Wasu masoya biyu da aka sace a ranar Lahadi, kasa da mako daya kafin daurin aurensu sun samu 'yanci a jihar Ekiti kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Majiyoyi sun ce an sako masayan biyu ne a wani daji kusa da Ayedun na jihar Ekiti a ranar Alhamis da yamma bayan an biya kudin fansa.

Masoya da aka yi garkuwa da su sun samu 'yanci ana jajiberin ɗaurin aurensu
Kwamishinan 'yan sandan jihar Ekiti, Tunde Mobayo. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Majiyoyin sun ce:

"An shirya fara yin bikin su ne a ranar Juma'a (yau), na amsa auren yayin da a ranar Asabar kuma za a daura auren."

Wani majiyar daban wanda ya ce masoyan suna cikin dimuwa tun bayan sako su daga hannun masu garkuwar ya ce ba za a yi auren a ranar Juma'a ba da Asabar kamar yadda aka tsara sai dai za a zabi sabon rana.

Ya ce:

"Ban ga ko daya daga cikinsu ba tun bayan dawowarsu amma bisa dukkan alamu sun shiga mawuyacin hali. Amma muna gode wa Allah tunda sun dawo lafiya."

Majiyar ya kara da cewa ba zai iya tabbatarwa ba ko an biya kudin fansa ko kuma ba a biya ba duk da cewa wasu na cewa an biya N1m wasu kuma sun ce N3m.

Masu garkuwa da mutanen sun kama masoyan ne a hanyar Ilasa Ekiti-Ayebode Ekiti a karamar hukumar Ekiti East yayin da suke dawowa daga Ado Ekiti inda suka tafi siyayyan kayan aure.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

'Yan sanda sun tabbatar da ceto su

Kakakin yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da sakin masoyan yana mai cewa:

"Eh, an sako su. An sako su ne sakamakon jajircewa daga yan sanda, sojoji, Amotekun, 'Yan Sakai da mafarauta."

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa an kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a lamarin, yana mai cewa ana tsare da su a hedkwatan 'yan sanda na Ado Ekiti kuma za a gurfanar da su da zarar an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel