Yadda Jami’an EFCC suka duro mani gida da duhun dare, suka yi mana ta’adi inji ‘Yar jarida

Yadda Jami’an EFCC suka duro mani gida da duhun dare, suka yi mana ta’adi inji ‘Yar jarida

  • Wata ‘yar jarida ta zargi jami’an EFCC da shigo mata gida da karfi da yaji yau
  • Norah Okafor tace da kimanin karfe 1:30 ta ji mutanen za su shigo mata daki
  • A cewarta an tafi mata da wasu kayanta, sannan an yi wa ‘yanuwanta duka

Nigeria - Wata ‘yar jarida mai suna Norah Okafor, ta bada labarin yadda wasu jami’an EFCC suka shigo mata gida dazu a lokacin da bai kamata ba.

Jaridar Daily Trust tace Norah Okafor ta zayyana duk abin da ya faru a shafinta na sada zumunta.

A cewar wannan ‘yar jaridar, jami’an hukumar ta EFCC sun shigo gidansu ne a ranar Alhamis 23 ga watan Satumba, 2021, da karfe 1:36 na tsakar dare.

Kara karanta wannan

‘Yan bindigan da aka fatattako daga Zamfara sun tare hanyoyin Katsina suna neman abinci

“Da karfe 1:36 na dare, danuwana ya fada mani cewa ‘yan fashi suna bakin kofar gidana, suna kokarin shigo wa.”
“Saboda an sa wayar wuta a samar katangar, ban damu ba, domin na yi tunanin babu yadda za ayi su iya zuwa ciki.”
“Ai kuwa na yi kuskure, karfe 2:00 daidai sai ga su a haraba. Sun zo a shiryensu, sun haura 25 a cikin motoci biyu.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Steel Gate
Wata kofar shiga gida Hoto: jiji-blog.com
Asali: UGC

Jami'an EFCC ko 'yan fashi da makami?

Norah Okafor tace jami’an sun yi shigar bakaken kaya, suka rufe jikinsu kamar ‘yan fashi. Okafor tace sun tafi da mubudan mota, wayoyi da komfutoci.

“Wani jibgege ya hau saman katangar, ya datse wayoyin, ya sauka da gatari ya faskare kofar shiga gidan, Daga nan suka shiga cikin dakin da na ke.”

Bayanan da tayi sun bayyana cewa jami’an na EFCC sun lakada wa ‘yanuwanta da makwabcinta duka, kuma suka yi yunkurin bude motocin cikin gidan.

Kara karanta wannan

Fani-Kayode: Abin da ya sa aka ji ni a APC duk da na yi wa Shugaba Buhari da wasu ta-tas a baya

Okafor tace wadannan mutane sun shafe sama da sa’a guda a cikin gidanta, suna ci mata mutunci. Inda ta gode wa Ubangiji, mahaifiyarta ba ta nan.

Matsalar 'yan bindiga

A ranar Laraba ne mai girma Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana abubuwan da suke jawo wa jihohi cikas a yaki da ‘yan bindiga da ake yi.

Rt. Hon Aminu Bello Masari yace Sojoji da ‘Yan Sanda ba su ba jihohin Arewa goyon baya da kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel