Fani-Kayode: Abin da ya sa aka ji ni a APC duk da na yi wa Shugaba Buhari da wasu ta-tas a baya

Fani-Kayode: Abin da ya sa aka ji ni a APC duk da na yi wa Shugaba Buhari da wasu ta-tas a baya

  • Femi Fani-Kayode ya kare kan shi bayan komawarsa jam’iyyar APC mai mulki
  • Tsohon Minisan yace ya rika caccakar Muhammadu Buhari ne a da a bisa jahilci
  • Fani-Kayode yace ba don APC ta canza ba, da ba za a ji shi a cikin jam’iyyar ba

Abuja - Tsohon Minisan harkokin jirgin sama, Femi Fani-Kayode, ya kare kan shi na koma wa APC bayan tsawon shekaru yana caccakar jagororinta.

Cif Femi Fani-Kayode yayi magana a gidan talabijin na Channels TV, inda ya yi karin haske a kan dalilin koma warsa jam’iyyar APC mai mulki daga PDP.

Da yake magana a shirin ‘Politics Today’, Cif Fani-Kayode yace ya rika sukar Muhammadu Buhari ne saboda a lokacin ya jahilci wanene shugaban kasar.

“Na rika magana game da Buhari ne daga waje, yanzu na san shi ciki-da-bai. Ba cewa nake yi mutumin kirki ba ne shi ko na banza.”

Kara karanta wannan

Yau ce rana mafi muni a tarihin siyasata, in ji hadimin Buhari yayin da Fani-Kayode ya koma APC

“APC da nake magana a kanta lokacin, ta banbamta da jam’iyyar da ake da ita yau. Mu maida hankali kan zaman lafiya da hadin-kai.”

Punch ta rahoto yadda aka tuna wa ‘dan siyasar wasu maganganun da ya yi a baya, inda har ya rika cewa gara ya mutu, da ya shiga jirgin jam’iyyar APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fani-Kayode
Femi Fani-Kayode da manyan APC Hoto; Femi Adesina
Asali: Facebook

Lauyan yace a yanzu shiga jam’iyyar APC ne mafita, duk da abin da wasu suke tunani a kasar nan.

“APC jam’iyya ce mai ra’ayi mai sassauci. Abubuwa da yawa sun faru a shekarun baya. Jam’iyyar ta canza, shugaban kasa ya karbi sauyin.”
“Da a ce ba a canza shugabannin jam’iyyar APC ba, da ba zan sauya-sheka zuwa jam’iyyar ba.”

Ina maganar PDP?

Haka zalika Daily Trust ta rahoto Kayode yana cewa yayi abin da ya dace da wannan mataki da ya dauka, ba tare da la’akari da surutun masoya ko makiya ba.

Kara karanta wannan

Sauya-sheka: Fani-Kayode, Matawalle da sauran ‘Yan siyasan da suka girgiza kowa da shiga APC

“Abubuwa sun faru a PDP, ba zan yi magana a kan jam’iyyar PDP a shirin nan ba, har sai sun takoli ni.”

FFK mayaudari ne - Gumi

A jiya aka ji babban Malamin addinin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa tuni ya san Femi Fani Kayode mayaudari kuma makaryacin banza ne.

Gumi ya tofa albarkacin bakinsa ne a kan sauya shekar da Fani-Kayode ya yi zuwa APC. Malamin ya yi maganar yadda 'dan siyasar ya rika zaginsa a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel