Kotu ta yanke wa mata ɗaurin shekaru 17 da aiki mai tsanani a gidan yari saboda babbaka mijinta da ruwan zafi

Kotu ta yanke wa mata ɗaurin shekaru 17 da aiki mai tsanani a gidan yari saboda babbaka mijinta da ruwan zafi

  • Kotu ta yanke wa wata mata shekaru 17 a gidan gyaran hali da horo mai tsanani saboda ta babbaka mijin ta da ruwan zafi
  • A ranar Laraba, wata kotun majistare dake Malawi ta yanke wa matar mai shekaru 20 hukuncin bayan tayi aika-aikar saboda wata rigima ta hada su
  • Rahotanni sun bayyana yadda mijin ya ki ba matar kudin da zata yi bikin rantsarwar agololin ta, hakan ya tunzura ta ta babbaka shi

Kasar Malawi - Kotu ta yanke wa wata matar aure daurin shekaru 17 a gidan gyaran hali da horo mai tsanani saboda ta babbaka mijin ta da tafasasshen ruwa kamar yadda LIB ta ruwaito.

Alkalin wata kotun majistare dake zama a Malawi a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba yanke wa wata mata mai shekaru 20, shekaru 17 a gidan gyaran hali da horo mai tsanani saboda ta babbaka mijin ta da ruwan zafi akan wata rigimar kudi da ta shiga tsakanin su.

Kara karanta wannan

'Yan sanda za su gurfanar da wata matashiya ‘yar shekara 25 da ke yi wa ‘yan bindiga leken asiri a Katsina

An yanke wa matar aure daurin shekaru 17 a gidan yari saboda antawa mijinta tafasashen ruwa
Matar aure da kotu ta yanke wa hukunci saboda antayawa mijinta ruwan zafi. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Sifeta Blessing Madikhula ta gabatar wa da kotu cewa wani Wilson Chimenya mai shekaru 34 ya auri Nunu Saidi a shekarar da ta gabata kuma ta zo gidan da agololin ta guda 3 wadanda ta rabu da mahaifin su.

A watan Yulin 2021, sun dan samu hayaniya da mijin ta saboda wata rigima wacce basu bayyana ba, har ta yi yaji ta bar gidan.

Ta kona shi ne saboda ya ki bata kudin hidimar rantsarwar agololin ta

Madikhula ta kara da cewa matar ta koma gidan ta a ranar 28 ga watan Augusta inda ta bukaci mijin ta ya taimaka mata da kudin bikin rantsarwar agololin ta.

Sai dai mijin ya ki bata ko sisi inda yace ba yaran sa bane don haka matar ta hassala.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: Mu ilmantar da 'yan Najeriya ko kuma su addabi kasa da manyan kasa

Daga nan suka fara fada har ya kai ga matar ta debi ruwan zafi daga kan wuta ta watsa wa mijin ta a baya sannan ta tsere ta bar shi a babbake.

Daga nan ne aka nufi asibitin Namwera da shi inda aka ga ya kone sosai

Da farko ta fara musanta zargin da ake mata, sai daga baya ta nemi afuwa

Matar ta bayyana a kotu inda ta musanta zargin da ake mata, daga nan ne ‘yan sanda suka binciko mutane 3 wadanda suka bayar da shaidar cewa ita ta aikata.

Bayan nan ne Nunu ta roki rangwame har tana cewa yaranta guda 3 zasu sha wahala idan aka tura ta gidan gyaran hali amma Madikhula ya tunatar da kotu cewa lokaci ya yi da mata za su daina cutar da mazajen su.

Madikhula ya kara da cewa yanzu ne kungiyoyin kare hakkin bil’adama su ka yi shiru, za su iya tayar da hankali idan su ka ji ba a dauki wani mataki akan ta ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Yayin yanke hukunci, Babban alkalin kotun majistare Rodrick Michongwe ya yanke mata hukuncin shekaru 17 a gidan gyaran hali don hakan ya zama darasi ga mata irin ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel