Ministan Buhari: Mu ilmantar da 'yan Najeriya ko kuma su addabi kasa da manyan kasa

Ministan Buhari: Mu ilmantar da 'yan Najeriya ko kuma su addabi kasa da manyan kasa

  • Ministan kwadago ya bayyana cewa, rashin ilimi ya haifar da mummunan matsala ga Najeriya
  • Ya ce idan ba a ilmantar da 'yan Najeriya to lallai kasar nan ba za ta kubuta daga matsala ba
  • Ya bayyana cewa, rashin ilimi ne ke jefa mutane cikin ta'addanci da aikata munanan ayyuka

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya ce hauhawar rashin aikin yi na kawo hadari ga Najeriya, Punch ta ruwaito.

Ya danganta rashin ilimi ga matsalolin da ke addabar kasar, yana mai gargadin cewa idan ba a yi maganin lamarin ba, kasar za ta iya “shafewa gaba daya.”

Ministan ya fadi haka ne a taron koli na tattalin arzikin hadin gwiwa da ma'aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci suka shirya a Abuja ranar Talata 14 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ba zamu iya kin yafewa 'yan bindiga ba, su ma 'yan Najeriya ne

Ministan Buhari: Mu ilmantar da 'yan Najeriya ko kuma su addabi kasa da manyan kasa
Chris Ngige, ministan kwadago | Hoto: punchng.com

An yiwa taron take da, 'Fassara Manufofin Ci Gaba mai Dorewa zuwa kasuwancin cikin gida a Najeriya.'

Ngige ya ce:

“Muna cikin matsala a matsayin kasa. Muna cikin matsala kuma duk wanda ya gaya muku bai san muna cikin matsala ba yana yi wa kansa karya ne kuma ya muku karya.

Ya bayyana cewa, idan aka ci gaba da zama da wadannan matsaloli, to lallai Najeriya za ta kara shiga damuwar da ta fi wanda ake ciki a yanzu kuma za ta shafi kowa har da manyan kasar nan.

Rashin ilimi ne yasa mutane ke fadawa ta'addanci

Da yake tsokaci kan bukatar samar da ingantaccen ilimi ga mutane tun daga tushe, ya ce rashin samar da irin wannan shine dalilin da ya sa aka rudar da mutane su shiga cikin tashin hankali, na ta'addanci da sauransu.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Ya kara da cewa:

“Idan ba ku kashe jahilci ba, za ku samar da mutanen da za su zama masu wankakkiyar kwakwalwa da za su yarda da Biyafara za ta magance musu duk matsalolinsu; Oduduwa, duk matsalolin su za su tafi, Boko Haram.
“Idan ba mu magance su ba, za mu ci gaba da haka har sai an ruguza wannan kasar gaba daya; ba mu yin addu’ar hakan. Dole ne mu ba mutane ilimi tun daga tushe.”

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda Ministan kasuwanci da saka hannun jari, Adeniyi Adebayo ya wakilta, ya bayyana kanana da matsakaitan masana'antu a matsayin kashin bayan tattalin arzikin Najeriya.

Abinda ya dace 'yan Najeriya su iiwa shugabannin da suka gaza cika alkawari, tsohon ministan sadarwa

Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Jerry Gana, yace ya kamata yan Najeriya su canza shugabanni da jam'iyyun siyasar da basu taɓuka komai a zaɓen 2023, kamar yadda This Day Live ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

A cewarsa, maimakon da nasani da bacin rai, kamata yayi yan Najeriya su saurari lokacin da ya dace a babban zaɓen dake tafe don hukunta shugabannin da suka gaza cika alkawurransu.

Gana ya faɗi haka ne a wata fira da manema labarai jim kaɗan bayan kaddamar da sabuwar cocin Anglican a Zone 5, Wuse Abuja, ranar Lahadi.

Shugabannin Boko Haram matsorata ne: Tubabben kwamandansu ya tona asiri

A wani labarin, Wani tsohon kwamandan ‘yan ta’addan Boko Haram, Adamu Rugurugu, ya ce ya yi watsi da ta’addanci ne sakamakon gano cewa akidar 'yan ta’addan Boko Haram zamba ce.

A cikin bidiyon da PRNigeria ta samu, kasurgumin dan ta'addan ya ce manyan shugabannin kungiyar a koyaushe za su aika su a kashe su ne a fagen daga, tare da yaudarar su cewa aljanna ce za ta zama makomar su idan an kashe su.

A cewar Mista Rugurugu, manyan shugabannin Boko Haram ba sa iya tunkarar sojoji sai dai buya daga baya suna amfani da mayakansu wajen kai hare-haren kan sojoji a arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

Asali: Legit.ng

Online view pixel