'Yan sanda za su gurfanar da wata matashiya ‘yar shekara 25 da ke yi wa ‘yan bindiga leken asiri a Katsina
- Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama matashiyar da ke kai wa ‘yan bindiga man fetur
- An tattaro cewa matashiyar wacce ake zargin mai suna Rashida Hussaini tana da hannu a ayyukan da suka shafi fashi da makami tare da karya dokar tsaro na Aminu Masari
- Hukumar ‘yan sandan ta ce za ta gurfanar da ita a gaban kotu, bayan ta gaza bayar da gamsasshen bayani a kan kanta
An kama wata mata 'yar shekara 25 da ake zargi da yi wa ‘yan bindiga leken asiri kuma 'yan sanda a jihar Katsina za su gurfanar da ita nan ba da jimawa ba, Channels TV ta ruwaito.
Wacce ake zargin mai suna Rashida Hussaini an ce tana da hannu a ayyukan da suka shafi fashi da makami tare da karya dokar tsaro da gwamnan jihar Aminu Masari ya sanya wa hannu kwanan nan.
'Yan sandan da ke sintiri na yau da kullum sun kama Rashida yayin da take kan hanyarta ta samar da mai ga 'yan ta'adda a ranar 14 ga watan Satumba, 2021, da misalin karfe 14:30 na rana a kan hanyar Kofar Guga zuwa Jibia.
An same ta dauke da buhu da kuma jakar leda dauke da galan uku kowannensu cike da mai, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya bayyana yayin gabatar da wacce ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Katsina.
SP Isah ya ce yayin da ake yi mata tambayoyi, wacce ake zargin ta gaza bayar da gamsasshen bayanin kanta.
Ya ce:
"Ta shaida wa jami'an 'yan sanda a lokacin da aka kama ta cewa ta fito ne daga kauyen Daddara a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina."
A cewarsa, ta canza kalaman nata, inda ta ce ta fito ne daga jihar Gombe kuma daga baya ta sake canzawa ta ce ta fito daga wani kauye da ake kira Hirji a Jamhuriyar Nijar.
Isah ya kara da cewa:
"Don haka a yanzu za mu tura ta gaban kotu saboda karya dokar tsaro da babban gwamnan jihar, Aminu Masari ya sanya wa hannu kwanan nan, da kuma hadin kai a cikin ayyukan da suka shafi fashi da makami."
An Cafke Hatsabibin Ɓarawon Shanu Da Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi a Jihar Katsina
A wani labarin, hukumar tsaro ta NSCDC ta ce ta damke wani wanda ake zargin barawon shanu ne da wani mai safarar miyagun kwayoyi a jihar Katsina, rahoton Daily Nigerian.
Jami’in hulda da jama’an hukumar na jihar, DSC Muhammed Tukur ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba a Katsina.
A cewar sa, daya daga cikin su shekarun sa 20 kuma mazaunin kauyen Maikaho ne dake karkashin karamar hukumar Jibia, ana zargin sa da satar shanu da kuma bai wa ‘yan bindiga bayanai.
Asali: Legit.ng