Sheikh Kabiru Gombe ya yafewa Muaz Magaji, sun gana ido da ido

Sheikh Kabiru Gombe ya yafewa Muaz Magaji, sun gana ido da ido

  • Bayan bada hakuri a Facebook, Muaz Magaji yayi takakkiya zuwa wajen Kabiru Gombe
  • Malamin yace ya yafe masa kuma yayi kira ga jama'a su yafe masa
  • Malam Gombe yace yanzu sun kulla zumunci da dan sarauniya

Abuja - Sakataren Janar na Jama'atu Izalatul Bid'a wa iqamatus-Sunnah, Malam Kabiru Haruna Gombe, ya bayyana cewa ya yafewa Muaz Magaji, tsohon kwamishanan ayyukan Kano.

Malam Gombe ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook da yammacin Asabar, 11 ga Satumba, bayan karban bakuncin Muaz Magaji.

Magaji yayi tattaki har zuwa gidan Malamin kuma ya gana da shi don bashi hakuri ido da ido.

Kabiru Gombe yace:

"A yammacin asabar dinnan tsohon kwamishinan ayyuka na jahar Kano, Honourable Muazu Magaji ya ziyarce mu a gida domin bada hakuri tare da janye kalamansa da yayi a shafinsa na Facebook. Ya kuma yi sa'a ya same mu da shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau.

Munyi hakuri, mun yafe masa, kuma mun kulla zumunci. Allah ya kiyaye gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ina kira ga sauran 'yan uwa abokan gwagwarmaya da kuma ku yafe masa, domin Allah yana son masu yafiya."

Sheikh Kabiru Gombe ya yafewa Muaz Magaji, sun gana ido da ido
Sheikh Kabiru Gombe ya yafewa Muaz Magaji, sun gana ido da ido Hoto: Muhammad Kabir Haruna
Asali: Facebook

Ya yi barazanar shigar da shi kotu

Zaku tuna cewa babban Malamin yayi barazanar shigar da tsohon kwamishanan Ganduje, Muazu Magaji kotu.

Kabiru Gombe ya yi watsi da maganar da Muazu Magaji ya daura a shafinsa na Facebook cewa ya nadi waya tsakanin Kabiru Gombe da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC.

A cewarsa, shi Malamin addini ne kuma bashi da alaka da wata jam'iyya a Najeriya kuma shi ba dan siyasa bane.

Muaz Magaji ya nemi gafara

Tsohon kwamishanan ayyukan Kano, Muaz Magaji wanda akafi sani da Win-Win Dan Sarauniya, ya nemi gafarar Malam a sakon da ya daura shafinsa na Facebook.

Ya ce ba shi ya kirkiri labarin ba, a wata jarida ya gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel