Ina ni ina ja da Malamai?, ina neman afuwarka Malam: Muaz Magaji ga Kabiru Gombe
- Dan Saurauniya Win-Win ya mika afuwa ta gaggawa ga Sheikh Kabiru Gombe
- Muaz Magaji ya bayyana cewa ba shi ya kirkiri labarin ba
- Ya ce kullum yana gujewa samun sabani da Malamai da Sarakunan gargajiya
Kano - Bayan barazanar shigar da shi kotu cikin sa'o'i 12 da babban Malami, Sheikh Kabiru Haruna Gombe yayi, tsohon kwamishanan ayyukan Kano ya nemi gafarar Malam.
Muaz Magaji wanda akafi sani da Win-Win Dan Sarauniya ya ce ba shi ya kirkiri labarin ba, a wata jarida ya gani.
Saboda haka yana neman afuwar Malam Kabiru Gombe yayi hakuri kada ya gurfanar da shi gaban kuliya.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook.
Muaz Magaji yace:
"Mallam Kabiru Gombe, sakon Allah wadai da kai kan labarin da na gabatar, ina mai baka hakuri da neman afuwa, kuma ina sanar dakai cewa ba nine na kirkiri labarin ba, Jaridar Punch Hausa ne suka buga shi.
Ina ganin yanzu ka fahimci hakan don naga anja hankalinka ga hakan, wallahi sam bana son Malami ko Sarki na fitar da ra'ayi kururu a siyasa irin tamu ta Nigeria don nasan illar da za ta iyayi mana a addinance da Al'adance, don haka nai sharing labarin don Jan hankali.
Amma in ba kai kayi wannan maganar ba to don Allah kayi hakuri, in kuma ajizan ci yasa kayi to a guji gaba don amana tayi karanci a siyasa."
Sheikh Kabir Gombe yayi barazanar shigar Muazu Magaji kotu kan kiransa dan APC
Sakataren Janar na Jama'atu Izalatul Bid'a wa iqamatus-Sunnah, Malam Kabiru Gombe, yayi barazanar shigar da tsohon kwamishanan Ganduje, Muazu Magaji kotu.
Kabiru Gombe ya yi watsi da maganar da Muazu Magaji ya daura a shafinsa na Facebook cewa ya nadi waya tsakanin Kabiru Gombe da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC.
A cewarsa, shi Malamin addini ne kuma bashi da alaka da wata jam'iyya a Najeriya kuma shi ba dan siyasa bane.
Kabiru Gombe yace: Wannan karya da ya kwantara min mai hade da cin mutunci mafi kololuwa a rayuwa, sam ba'a yita ba, bamu da alaka da duk wani mai mulki da ya wuce alaka ta addini."
Asali: Legit.ng