Sheikh Kabir Gombe yayi barazanar shigar Muazu Magaji kotu kan kiransa dan APC

Sheikh Kabir Gombe yayi barazanar shigar Muazu Magaji kotu kan kiransa dan APC

  • Wata sabuwa ta bayyana tsakanin Malam Kabiru Haruna Gombe da Muazu Magaji
  • Malam Gombe ya zargi Muaz Magaji da yi masa sharrin zama dan APC
  • Kabiru Gombe ya yi watsi da maganar inda yace shi ba dan siyasa bane

Abuja - Shahrarren Malamin addini kuma Sakataren Janar na Jama'atu Izalatul Bid'a wa iqamatus-Sunnah, Malam Kabiru Gombe, yayi barazanar shigar da tsohon kwamishanan Ganduje, Muazu Magaji kotu.

Kabiru Gombe ya yi watsi da maganar da Muazu Magaji ya daura a shafinsa na Facebook cewa ya nadi waya tsakanin Kabiru Gombe da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC.

A cewarsa, shi Malamin addini ne kuma bashi da alaka da wata jam'iyya a Najeriya kuma shi ba dan siyasa bane.

A martanin da ya saki a shafinsa na Facebook, babban Malamin yace:

Kara karanta wannan

Ina ni ina ja da Malamai?, ina neman afuwarka Malam: Muaz Magaji ga Kabiru Gombe

"Ni Muhammad Kabir Haruna Gombe, nayi Allah wadai da karya da wani bawan Allah daga jihar Kano mai suna Muaz Magaji ya kirkira kuma ya jingina ta gareni. Kamar yadda yace nayi waya da Gwamna Mai Mala Buni akan maganar siyasa, ni tunda nake ban taba waya da Mai Mala Buni ba ko akan menene, domin wannan ba shine a gaban mu ba.
Mu ba 'yan siyasar jam'iyya bane, bamu da jam'iyya a siyasa, illa kawai muce da jama'a su zabi wanda mukewa zaton mutumin kirki ne, in zabe yazo mu cewa jama'a su zabeshi, ballatana har nayi barazanar fita daga wata jam'iyya zuwa wata jam'iyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan karya da ya kwantara min mai hade da cin mutunci mafi kololuwa a rayuwa, sam ba'a yita ba, bamu da alaka da duk wani mai mulki da ya wuce alaka ta addini."

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

Malam Kabiru Gombe ya ce idan Muazu Magaji bai janye sharrinsa da ya masa cikin awanni 12 ba, za'a makashi gaban kuliya.

Yace:

"Dan haka mun baiwa wannan mutum mai suna Muazu Magaji awanni goma sha biyu (12hours) da ya fito ya janye maganarsa ko mu kai kara zuwa kotu, Dan Baza mu saka ido a wannan karya da ya mana tare da cin mutunci ya tafi a banza ba matukar bai fito ya karyata kansa ba."

Me Muazu Magaji yace?

Tsohon kwamishanan ayyuka na jihar Kano, Muaz Magaji, ya bayyana cewa ya nadi magana tsakanin Kabiru Gombe da Mai Mala Buni cewa ba zasu yarda Kwankwaso ya shiga APC ba.

Sheikh Kabir Gombe yayi barazanar shigar Muazu Magaji kotu kan kiransa dan APC
Sheikh Kabir Gombe yayi barazanar shigar Muazu Magaji kotu kan kiransa dan APC
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel