Ni Soja ne, Likita kuma Malami mai Digiri 3, saboda haka ba zan yi shiru ba: Sheikh Gumi

Ni Soja ne, Likita kuma Malami mai Digiri 3, saboda haka ba zan yi shiru ba: Sheikh Gumi

  • Sheikh Ahmad Gumi yayi martani ga mai magana da yawun shugaban kasa
  • Malamin yace shi kwarraren Likita ne kuma Soja saboda haka ya san abinda yake fada
  • Gumi ya shahara da tofa albarkacin bakinsa kan lamarin tsaro a Najeriya

Kaduna - Shahrarren Malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya sake kira ga gwamnatin tarayya cewa ta rungumi sulhu da yan bindiga saboda yaki ba zai kawo karshen matsalar tsaro ba.

Gumi yace al'ummar jihar Zamfara da ake artabu yanzu da yan bindiga kawai ke shan wahala saboda tuni yan bindigan sun gudu, kamar yadda ya daura a shafinsa na Facebook.

Ya ce yan bindigan yanzu sun fara shiga garuruwan da ko hanya basu sani ba amma duk da haka suna cigaba da aikata laifin garkuwa da mutane saboda haka korarsu daga Zamfara ba zai yi amfani ba.

Kara karanta wannan

Magashi: 'Yan fashin daji sun zama fitina, 'yan Najeriya ba su yarda za mu iya maganinsu ba

Yace:

"La'lla baku samu labarin cewa yan bindiga tuni sun samar da hanyoyin tserewa ruwan bama-baman Sojoji. Sun fada mana cewa sai dai ku kashe matanmu da yaranmu da hare-harenku."
"Jiya (Alhamis), wasu gungun mutane biyu da harin yan bindiga ya shafa sun fada min cewa an sace yan uwansu a Kaduna - Rigachikun da Keke. Wani Injiniya da ya samu tsira yace da ya saurari yan bindigan ya fahimci cewa baki ne saboda yaji suna tambayar mutan gari hanya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Maganar gaskiya Zamfara ta musu zafi yanzu, amma zasu koma wasu wurare. Shin za'a yanke duka hanyoyin sadarwa a Najeriya ne?."
Yayinda yake kara kira ga hukuma tayi sulhu da yan bindiga, yace "Yaki bai taba zama mafita ba a ko ina."

Ni Soja ne, Likita kuma Malami mai Digiri 3, saboda haka ba zan yi shiru ba: Sheikh Gumi
Ni Soja ne, Likita kuma Malami mai Digiri 3, saboda haka ba zan yi shiru ba: Sheikh Gumi Hoto: Dr Ahmad Gumi
Asali: UGC

Malam Gumi yayi martani ga mai magana da yawun shugaban kasa kan kalamansa na cewa yana tausayawa yan bindiga.

Kara karanta wannan

Da na sani ban yiwa yan bindiga afuwa a baya ba, Gwamna Aminu Masari

Gumi yace shi Malamin addini ne mai digri 3, shi Likita ne kuma tsohon Soja; saboda haka don soyayyar kasa da al'umma yake abubuwan da yakeyi.

Me fadar Shugaban kasa ta ce ga Sheikh Gumi?

Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya kalubalanci fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, kan cewa da yayi farmakin da sojoji ke kaiwa zai kara munana ta'addanci a Najeriya.

Adesina a cikin wani wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba ya bayyana Gumi a matsayin “mai son yan fashi da makami ”

Asali: Legit.ng

Online view pixel