Magashi: 'Yan fashin daji sun zama fitina, 'yan Najeriya ba su yarda za mu iya maganinsu ba

Magashi: 'Yan fashin daji sun zama fitina, 'yan Najeriya ba su yarda za mu iya maganinsu ba

  • Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce 'yan bindiga sun zama fitina a yankunan arewa maso yamma da ta tsakiya
  • A cewarsa, 'yan Najeriya sun fitar da tsammanin cewa gwamnatin za ta iya maganinsu, amma a zuba ido a gani
  • Magashi ya ce babu shakka tsaro alhakin dukkan gwamnatoci ne da kuma jama'ar Najeriya baki daya

Aso Villa - Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce 'yan bindiga suna tada hankula a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

TheCable ta ruwaito cewa, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bukatar a gaggauta magance matsalar su.

Ministan ya sanar da hakan a ranar Talata bayan taron majalisar tsaro da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Villa, Abuja.

Magashi: 'Yan fashin daji sun zama fitina, 'yan Najeriya ba su yarda za mu iya maganinsu ba
Bashir Magashi tare da hafsoshin tsaron kasa yayin taron majalisar tsaro. Hoto daga Thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yakar 'yan bindiga: Ba mu sukar matakan tsaro da gwamnati ta dauka, Dattawan Arewa

"Wannan taron an kira shi ne domin tattauna wa kan lamurran da ke faruwa yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya. Mun yi magana kan cigaba, matsaloli da duk wani abinda ya shafi ta'addanci, satar jama'a da 'yan fashin daji.
"Daga taron, mun yadda cewa abubuwan da ke faruwa a jihar Zamfara da arewa ta tsakiya matsala ne ga gwamnati kuma dukkan cibiyoyin ta ke da alhakin magance su.
“Mun tattauna kan bukatar gaggawa ta shawo kan matsalar 'yan bindiga. Mun yadda cewa sun zama fitina, suna kashe jama'a, suna yin abinda suke so tare da fadin duk abinda duk suke so
“Mun yadda cewa mun yi nisa wurin tabbatar da hadin kan kasar nan. Idan aka duba baya kamar 2014, za ku gane cewa akwai cigaba, amma jama'a ba su ganin hakan.
"Ta yuwu basu yadda cewa za mu iya wani abu bane ko kuma akwai abinda ba za mu iya ba, amma muna kokarin gano me yasa mutane ba su gode wa gwamnati.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

“Mun san za mu iya, za mu iya amma muna bukatar goyon bayan kowanne dan Najeriya domin mu tabbatar da cewa mun kubuta."

A yayin taron, shugaban kasa ya daura alhakin samar da hanyoyin da za a shawo kan matsalar tsaron kasar nan kan hafsoshin tsaro, TheCable ta ruwaito.

Ce musu na yi ina da aure: Macen Kirista mai zaman zuhudu da aka sace yayin harbin Sowore ta bada labari

A wani labari na daban, Reverend Sister Emmanuella Ayanwu mai shekaru 34, daya daga cikin mutane 5 da masu garkuwa da mutane suka sata har suna kashe kanin Omoyele Sowore, kanin mai Sahara Reporters, ta bayyana yadda ta tsere daga hannun su.

Daily Trust ta ruwaito cewa, sun harbe kanin Sowore har lahira ya na hanyarsa ta zuwa jami’ar Igbinedion Okada da ke jihar Edo a ranar Asabar.

Kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana, sun harbe shi ne yayin da ya yi yunkurin tserewa daga masu garkuwa da mutanen da ke kan titin Benin zuwa Legas.

Kara karanta wannan

Yadda matashi a Gombe ya dale karfen sabis ya ce ba zai sauko ba sai an masa aure

Asali: Legit.ng

Online view pixel