Yan kabilar Igbo ke rike da tattalin arzikin Najeriya, saboda me zasu bar kasar: Shugaba Buhari

Yan kabilar Igbo ke rike da tattalin arzikin Najeriya, saboda me zasu bar kasar: Shugaba Buhari

  • Buhari ya samu muhimman karramawa daga wajen shugabannin yankin Igbo
  • Shugaban kasan ya kai ziyara jihar Imo ranar Alhamis, 9 ga Satumba
  • Buhari yace yana mamakin dalilin da zai sa yan kabilar su rika tunanin ballewa daga Najeriya

Imo - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kabilar Igbo a matsayin wadanda ke rike da akalar tattalin arzikin Najeriya saboda haka yana mamaki ace sunA son ballewa.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda ya kai ziyarar kaddamar da titunan da aka kammala a jihar Imo karkashin gwamna Hope Uzodinma na jihar.

Yace abu mafi muhimmancin ga Ƴan kabilar Ibo Shine, babu wani gari dazaka ziyarta a Najeriya ba tare da ganin Dan kabilar Ibo wa lau jagora akan abun more rayuwa ko kamfanin samar da magani.

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

Buhari yace:

"A saboda haka, abinda mamaki ne gare ni cewa Dan Kabilar Ibo ya dauki kanshi cewa shi ba wani sashe na Najeriya ne ba.
"Hujjoji na Nan fa kowa don su gani cewa Dan kabilar Ibo suke Manyan jagorori a tattalin arzikin Najeriya."

Yan kabilar Igbo ke rike da tattalin arzikin Najeriya, saboda me zasu bar kasar: Buhari
Yan kabilar Igbo ke rike da tattalin arzikin Najeriya, saboda me zasu bar kasar: Shugaba Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Buhari ya kara da cewa babu wata kasa da zata samu wani cigaban azo a gani ba tare da samun manyan aiyukan gina ƙasa ba.

Hakazalika, Ya yi Alkawari cewa, Gwamnatin Tarayya zata kammala aiyukan da take aikatawa a yankin Kudu maso Gabas, ciki harda Babbar Gada na (2nd Niger Bridge) dama kuma layin dogo daya kara de da hada Shiyar da Sauran sassan Kasar.

Zan taimakawa jihar Imo wajen magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari

Kara karanta wannan

Buhari: Igbo ne ke riƙe da tattalin arzikin Nigeria, sun fi iya kasuwanci

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya yi alkawarin taimakawa gwamnan jihar imo, Hope Uzodinma, wajen kawo cigaba a jiharsa ta hanyar samar da ayyuka.

Hakazalika Buhari ya bada tabbacin cewa zai yi amfani da ikonsa wajen taya gwamnan magance matsalar tsaro.

Buhari, wanda yayi magana yayin kaddamar da titin Egbeada-Onitsha a Owerri, yace ya gamsu gaskiya a ayyukan da gwamnan yayi, rahoton Punch.

Yace babu al'ummar da zata samu cigaba idan babu ayyukan jin dadin al'umma da tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel