Zan taimakawa jihar Imo wajen magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari

Zan taimakawa jihar Imo wajen magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari

  • Shugaba Buhari yayi alkawarin taimakawa gwamnan Imo wajen ayyuka da tsaro
  • Buhari ya kaddamar da manyan ayyukan da gwamnan yayi a jihar
  • Matasan APC sun baiwa Shugaba Muhammadu Buhari kyakkyawan tarba a Imo

Imo - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya yi alkawarin taimakawa gwamnan jihar imo, Hope Uzodinma, wajen kawo cigaba a jiharsa ta hanyar samar da ayyuka.

Hakazalika Buhari ya bada tabbacin cewa zai yi amfani da ikonsa wajen taya gwamnan magance matsalar tsaro.

Buhari, wanda yayi magana yayin kaddamar da titin Egbeada-Onitsha a Owerri, yace ya gamsu gaskiya a ayyukan da gwamnan yayi, rahoton Punch.

Yace babu al'ummar da zata samu cigaba idan babu ayyukan jin dadin al'umma da tsaro.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

"Na zagaya kuma na gamsu da abubuwan da na gani. Duk al'ummar da ba tada tsaro da ayyukan jin dadi ba zata cigaba ba, kuma ra'ayi na ya hadu da na gwamnan jihar Imo."
"Zan yi amfani da karfi na kundin tsarin mulki ta bani wajen taya gwamna yin nasara."

Zan taimakawa jihar Imo wajen magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari
Zan taimakawa jihar Imo wajen magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari Hoto
Asali: Facebook

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Owerri, jihar Imo

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Owerri, babbar birnin jihar Imo da safiyar Alhamis, 9 ga watan Satumba, 2021.

Buhari ya amsa gayyatar da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, yayi masa domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatinsa ta kammala.

Daga cikin wadanda suka tarbi shugaba Buhari akwai gwamnan jihar Ebonyi da manyan jami'an gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel