Buhari: Igbo ne ke riƙe da tattalin arzikin Nigeria, sun fi iya kasuwanci

Buhari: Igbo ne ke riƙe da tattalin arzikin Nigeria, sun fi iya kasuwanci

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kabilar Ibo mutane ne masu tarin fasaha da kirkire-kirkire
  • A cewar sa hankalin sa da tunanin sa ba za su taba gwada masa cewa 'yan kabilar za su iya rabuwa da Najeriya ba
  • Shugaban kasan ya ce tabbas kabilar su na bada gudumawa wurin habaka tattalin arzikin kasar nan

Jihar Imo - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kabilar Ibo su na da fasaha tare da iya kirkire-kirkire, saboda hakan ne kuwa suke bada gudumawa mai tarin yawa wurin habaka tattalin arzikin kasar nan, The Cable ta ruwaito.

Shugaban kasan ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taro da ya yi da shugabannin kudu maso gabas yayin ziyarar kwana daya da ya kai jihar Imo.

Kara karanta wannan

Na ga abubuwan da suka tabbatar da mutuncin Uzodinma, cewar Buhari yayin da ya kaddamar da ayyuka a Imo

Buhari: Igbo ne ke riƙe da tattalin arzikin Nigeria, sun fi iya kasuwanci
Hoton ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari a Imo. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya yi taron sirri da shugabannin kudu maso gabas.

Kamar yadda takardar da Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar, shugaban kasan ya bukaci shugabannin kudu maso gabas da su wayar da kan mutanen su kan bukatar aiwatar da zabe na adalci da gaskiya a 2023.

Ya ce:

"Ginshikin abu game da kabilar Ibo shi ne babu garin da za ka ziyarta a Najeriya ba tare da ganin wani wuri da suke rike da shi ba kama daga wurin siyar da magunguna ko wata ma'aikata. Don haka ban isa in yi tunanin cewa akwai wani Ibo da zai taba tunanin shi ba dan Najeriya ba ne.
"Babbar shaida ne da kowa ke iya gani kan cewa Ibo su ne ke rike da tattalin arzikin Najeriya."

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

A yayin alkawarin tabbatar da tsaro, shugaban kasan ya ce mulkinsa ya mayar da hankali wurin yaki da rashawa.

Jajiberin zuwan Buhari Imo: Gwamnatin jiha ta ja kunnen 'yan IPOB da kakkausar murya

Tunda farko, kun ji cewa gwamnatin jihar Imo ta ja kunnen 'yan IPOB a kan su tsaya a mazauninsu yayin kai ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ana sa ran a ranar Alhamis shugaban kasan zai kaddamar da wasu ayyukan Gwamna Hope Uzodinma.

An samu rahotanni a kan yadda IPOB ta bai wa mutanen ta umarnin zama a gida a ranar Alhamis, inda suke cewa ba su bukatar shugaban kasa a wani bangare na kudu maso gabas, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel