Da duminsa: Gwamnatin Kaduna ta sanar da sabuwar ranar bude makarantu

Da duminsa: Gwamnatin Kaduna ta sanar da sabuwar ranar bude makarantu

  • Gwamnatin jihar Kaduuna ta sanar da ranar komawa makaratun jihar da ta rufe saboda matsalar tsaro
  • Kamar yadda kwamishinan ilimi na jihar ya sanar, za a fara komawa ranar Lahadi, 12 ga watan Satumba
  • Sai dai kuma, ya ce za a koma zangon karatu na farkon 2021/2022 kuma za a yi kome kashi-kashi ba gaba daya ba

Kaduna- Gwamnatin jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yamma ta Najeriya a ranar Alhamsi ta saki sabon jadawali na komawar dalibai makarantu a fadin jihar bayan kwashe watanni da suka yi suna zaman gida sakamakon kalubalen tsaro.

Kwamishinan ilimi na jihar, Shehu Makarfi, ya bayyana hakan yayin da ya halarci taron bita ta yanar gizo wanda kungiyar malamai marubata ta Najeriya ta shirya, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rai da buri: Wani dattijo ya fashe da kuka, ya ce burinsa ya koyi ABCD kafin ya koma ga Allah

Da duminsa: Gwamnatin Kaduna ta sanar da sabuwar ranar bude makarantu
Da duminsa: Gwamnatin Kaduna ta sanar da sabuwar ranar bude makarantu
Asali: Original

Sabon jadawali

Kamar yadda Makarfi ya sanar, daliban za su fara komawa makarantu a ranar Lahadi, 12 ga watan Satumban 2021, Premium Times ta ruwaito.

Sai dai kuma, kwamishinan ya ce a maimakon komawa a fara zangon karatu na uku kamar yadda aka yi a jihar, za a koma makarantu ne domin a fara zangon karatu na farko na shekarar 2021/2022.

Ya kara da cewa, jihar ta riga ta tsara yadda za ta tabbatar da ana karasa karatun zango na ukun ta kafafen yada labarai.

Ya ce za a koma makarantun ne kashi-kashi ba a lokaci daya ba.

Zamfara: Gwamnati ta kwace kayan abinci da man fetur da aka yi yunkurin kai wa 'yan fashin daji

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta tare wasu motoci dauke da kayan abinci, abubuwan sha da kuma man fetur da suke yunkurin kai kayan sansanonin 'yan fashin daji a jihar.

Kara karanta wannan

Kiwo a fili: A ba mu lokaci mu horar da Fulani makiyaya, Miyetti Allah ta roki Legas

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, gwamnatin Zamfara ta ce ta damke a kalla mutum 100 da suka karya dokar kulle da Gwamna Bello Matawalle ya saka a jihar domin yaki da ta'addanci.

Sakataren jihar na kwamitin ayyuka na musamman a fannin tsaro, Abdulrasheed Haruna, ya sanar da hakan ga manema labarai a Gusau, ranar Laraba.

Matawalle ya kafa kwamiti na musamman na tabbatar da dokar domin a kiyaye ta duk don shawo kan matsalar tsaro na satar mutane tare da karbar kudin fansa da kuma satar shanu da ake fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel