Zamfara: Gwamnati ta kwace kayan abinci da man fetur da aka yi yunkurin kai wa 'yan fashin daji

Zamfara: Gwamnati ta kwace kayan abinci da man fetur da aka yi yunkurin kai wa 'yan fashin daji

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta yi caraf da wasu motoci dauke da kayan abinci, abubuwan sha da kuma man fetur dankare
  • An gano cewa motocin na yunkurin kai wa 'yan fashin daji kayan bukata ne a sansanoninsu da ke fadin jihar
  • Hakazalika, gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da damke a kalla mutum 100 da suka karya dokar kullen da aka saka a jihar

Gusau, Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta tare wasu motoci dauke da kayan abinci, abubuwan sha da kuma man fetur da suke yunkurin kai kayan sansanonin 'yan fashin daji a jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, gwamnatin Zamfara ta ce ta damke a kalla mutum 100 da suka karya dokar kulle da Gwamna Bello Matawalle ya saka a jihar domin yaki da ta'addanci.

Kara karanta wannan

Kisan Jos: Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari

Sakataren jihar na kwamitin ayyuka na musamman a fannin tsaro, Abdulrasheed Haruna, ya sanar da hakan ga manema labarai a Gusau, ranar Laraba.

Zamfara: Gwamnati ta kwace kayan abinci da man fetur da aka yi yunkurin kai wa 'yan fashin daji
Zamfara: Gwamnati ta kwace kayan abinci da man fetur da aka yi yunkurin kai wa 'yan fashin daji. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Matawalle ya kafa kwamiti na musamman na tabbatar da dokar domin a kiyaye ta duk don shawo kan matsalar tsaro na satar mutane tare da karbar kudin fansa da kuma satar shanu da ake fuskanta a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar 26 ga watan Augusta, gwamnan jihar ya saka hannu a dokar wacce ke da alaka da sashin kundin tsarin mulki na 1999 na Najeriya, Daily Nigerian ta ruwaito.

A yayin saka hannu a kan dokar, gwamnan ya ce ya yi aiki ne da karfin ikon da sashi na biyar, sakin layi na 2, sashi na 176, sakin layi na 2 da kuma sashi na 315, sakin layi na 2 na kudun tsarin mulki na Najeriya suka ba shi.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke dan bautar kasa da ke safarar alawa mai bugarwa daga UK

Ya ce, ya yi amfani da wannan karfin ikon na shi ne wurin kokarin ganin ya bai wa rayuka da kadarorin jama'ar jihar Zamfara kariya tare da shawo kan kalubalen tsaron da ya addabi jihar.

Zamfara: 'Yan fashin daji sun mayar da ajujuwar makarantu mafakarsu

A wani labari na daban, 'yan fashin daji da ke addabar jama'a mazauna Zamfara kuma fitinarsu ta sa aka rufe makarantu a jihar, sun fara mayar da ajujuwan makarantu zuwa mafakarsu a jihar arewa maso yamman.

Daily Trust ta binciko yadda makarantun firamare masu yawa a yankunan karkarar da suka addaba suka zama wurin kwanan 'yan ta'addan.

Tun baya, malamai da dalibai sun tattara komatsansu sun koma gida sakamakon al'amuran miyagun da ya hana su sakat.

Asali: Legit.ng

Online view pixel