Rai da buri: Wani dattijo ya fashe da kuka, ya ce burinsa ya koyi ABCD kafin ya koma ga Allah

Rai da buri: Wani dattijo ya fashe da kuka, ya ce burinsa ya koyi ABCD kafin ya koma ga Allah

  • Wani dattijo ya bayyana bukatarsa ta komawa neman ilimin boko kafin ya koma ga rabbana
  • A cewarsa, rashin zuwa makaranta da ya yi lokacin da yake yaro ya matukar cutar da shi
  • Ya kuma bayyana cewa, ya ga fa'idojoji da dama kan wadanda suka yi karatu kasancewarsu sa'anninsa

Wani dan Najeriya, Mallam Sani Muazu, ya sharbi kuka yayin da yake cewa yana son ya ilmantu kafin ya wucewarsa kiyama.

A cewar BBC News Pidgin, dattijon dan shekaru 62 bai taba zuwa makaranta ko neman ilimi ta kowane fanni ba kuma don haka, ba zai iya karanta haruffa daidai ba.

An gan shi rike da littafi da alkalami, inda ya nuna bacin ransa cewa rashin ilimi ya sa sace masa damarmaki da yawa a rayuwarsa.

Rai da buri: Wani dattijo ya fashe da kuka, ya ce burinsa ya koyi ABCD kafin ya mutu
Dattijo mai son komawa makaranta | Hoto: @bbcnewspidgin, blog.unicef
Asali: Instagram

Mallam Sani ya kara da cewa duk da mallakar wayar hannu, ba zai iya amfani da ita yadda ya kamata ba saboda rashin samun wadataccen ilimi kwata-kwata.

Mutumin ya ce ya ga fa'idodin yin karatu a rayuwar abokan kuruciyarsa da suka je makaranta.

Ya kuma bayyana sha'awarsa da niyyar rungumar duk wata dama ta ilimin da za ta zo masa kafin ya koma ga Allah.

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

Bayan shekaru 35 yana hidimar aikin gwamnati a matsayin malamin makaranta a jihar Borno, wani dan Najeriya ya koma talla a kan titi don samun abin biyan bukata.

An ga Al-Amin Shettima Bello wanda ya yi ritaya daga aikin koyarwa yana tafe yana tallan man zafi da aka fi sani mantileta a Maiduguri, Daily Post ta ruwaito.

Hanyar da Bello ke bi wajen samun na abin ka ya kasance yana zama a kusa da cibiyar ATM ta Bankin First Bank a Monday Market ta Maiduguri don kwastomomi daga masu zuwa da banki ko ATM.

An ga shaidar bayansa a wani faifan bidiyo da cibiyar sadarwa ta G-Role Africa ta yada a Facebook.

Abinda ka raina: Ana sayar da jakar 'Ghana-Must-Go' N860k a Amurka

A wani labarin, Hoton mashahuriyar jakar nan da matafiya ke saye don shake ta da kaya wato 'Ghana must go' ya bazu a yanar gizo inda jama'a ke martani kan yadda aka bayyana darajar kudi na jakar.

Lamarin ya girgiza jama'a da dama a kafar sada zumunta lokacin da aka ga an makalawa jakar farashi $2090 (N860,390.30) a wani shagon sayayya na yanar gizon mai Balenciaga na kasar Amurka.

Legit.ng ta leko wannan rubutun da wani mai suna @kennytrip2 ya wallafa a shafin sada zumunta tare da taken:

"Dakata .. meye? Shin ya kamata mu gaya musu?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel