IGR: Karancin kudi daga Gwamnatin Tarayya zai iya jawo wasu jihohi 8 su gurgunce a Najeriya

IGR: Karancin kudi daga Gwamnatin Tarayya zai iya jawo wasu jihohi 8 su gurgunce a Najeriya

  • Alkaluman Viability Index sun nuna wasu jihohi suna fuskantar barazana
  • Wadannan jihohin ba su samun kudin-shiga a shekarar 2020 da ta wuce ba
  • Irinsu Legas, Ribas, Oyo da Ogun sun tattara abin da ya fi karfin na jihohi 30

The Economic Confidential ta fitar da rahoton Viability Index watau ASVI da ya bayyana cewa jihohi takwas sun shiga halin ha’ula’i a Najeriya.

Wadannan jihohi suna fama da matsalar kudin-shiga idan aka kamanta da abin da suka samu a 2020.

Alkaluman sun nuna idan aka cire kason da ake ba gwamnonin jihohin daga asusun FAAC, ba su iya tatsar arzikin da zai rike su daga asusun IGR.

Gwamnatocin jihohin suna samun kudin-shiga ne daga tsarin harajin PAYE, harajin hanya da kuma kudi daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Legas ta yi zarra a Najeriya

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa sun fadi ainihin dalilin tsige su Nanono, sun ce ba don Allah aka yi ba

Naira tiriliyan 1.3 ne kudin-shigan da jihohin kasar nan 36 suka samu a shekarar 2019 da 2020. Daga ciki jihar Legas kadai ta samu Naira biliyan 418.

Abin da hakan yake nufi shi ne Legas kadai ta samu kudin IGR na jihohi 22 a dunkule. Ta biyu a jerin jihohin da suka fi samun kudi ita ce jihar Ribas.

Gwamnoni
Buhari da wasu Gwamnoni Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Yayin da Ribas ta samu Naira biliyan 117 a shekarar bara. Jihohin Kaduna Ogun sun samu Naira biliyan 50, yayin da Oyo ta iya tara Naira biliyan 38.

Jihar da take ta gaba a jerin IGR ita ce Anambra wanda ta samu Naira biliyan 28 a shekarar bara.

Wadannan jihohi shida da suka fi tattara IGR sun samu Naira biliyan 695. Idan aka tattara ragowar jihohin 30, abin da suka samu Naira biliyan 600 ne.

Kara karanta wannan

Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara

Jihohi 8 ba su da IGR mai tsoka

Akwai jihohi takwas da ba za su iya rayuwa ba da gudumuwar asusun tarayya ba. IGR dinsu bai kai 10% na abin da suke samu daga asusun FAAC ba.

Jaridar Daily Trust tace wadannan jihohi da suke fuskantar barazana sun hada Bayelsa wanda Naira biliyan 12 ta iya tatsa a kaf shekarar da ta wuce.

Bayan nan kuma sai jihohin Jigawa da Katsina da Naira biliyan 8.6 da Naira biliyan 11.3 kadai ya iya shiga cikin asusunsu, akasin kasonsu na FAAC.

Naira biliyan 8.3 kadai ya shiga asusun gwamnatin Yobe a 2020. Sauran jihohin da ke wannan rukuni su ne Neja, Taraba da Benuwai, duk a Arewa.

Badakalar NDDC

A baya an ji Abubakar Malami yace Gwamnatin Tarayya za ta shiga kotu da wadanda suke yin sama da fadi da kudin al'umma ta karkashin NDDC.

Ministan ya bayyana cewa duk wani wanda ya ci kudi a badakalar da aka yi a Hukumar NDDC zai yi amansu, kudin da aka wawura sun haura N6bn.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel